Zulum ya zauna a sashen talakawa na jirgin sama, ya dauki hoto da jama'a

Zulum ya zauna a sashen talakawa na jirgin sama, ya dauki hoto da jama'a

- Yan Najeriya a shafin soshiyal midiya sun jinjina wa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a kan kasantar da kai da kuma tsarin shugabancinsa

- An gano gwamnan kwanan nan zaune a sashen talakawa na cikin wani jirgin sama na kasuwa

- Da suke nuna gamsuwa da tsarin shugabancinsa, wasu yan Najeriya a soshiyal midiya sun bukaci gwamnan da ya nemi takarar Shugaban kasa a 2023

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya sa mutanen soshiyal midiya muhawara bayan an gano shi yana tarayya da fasinjoji masu karamin karfi a wani jirgin kasuwa.

Da ta wallafa wasu hotunan gwamnan tare da sauran fasinjoji a shafin Twitter, wata yar Najeriya mai suna Omasoro Ali Ovie ta rubuta:

“Zulum ya tsaya domin yin hoton selfie, kamar yadda fasinjoji suka bukata a hanyarsa ta zuwa gida daga Abuja. Yawancin gwamnoni kan dauki jirgi masu zaman kansu domin yin tafiya makamancin wannan, amma shi ya yi amfani da jirgin kasuwa sannan ya yi tarayya da talakawa masu karamin karfi.”

KU KARANTA KUMA: Gidajen Katsina da Barebari sun kai wa sabon Sarkin Zazzau gaisuwar ban-girma

Yan Najeriya a shafin sun je sashin sharhi na wallafar domin nuna ra’ayinsu a kan abunda gwamnan yayi.

Zulum ya zauna a sashen talakawa na jirkin sama, ya dauki hoto da jama'a
Zulum ya zauna a sashen talakawa na jirkin sama, ya dauki hoto da jama'a Hoto: @OvieSheikh
Asali: Twitter

Wani wallafa da mai suna @Ayokiitan1 yayi, ya ce: “ina kaunar yadda yake saukaka jagoranci. Da mutane irin Gwamna @ProfZulum a siyasar yau, akwai burin samun inganci gobe. Ina ta kallon tsarin tafiyar da abubuwansa na dan tsawon lokaci, kuma zuwa yanzu, “yana kokari sosai”

Wani shafi mai suna @stPaul51901553 ya ce: “Kusantan masu zabe, mutane abu ne mai kyau. Ina fatan mutanen wannan jirgi suna kokarin fada masa tunaninsu game da Borno da kuma yadda suke ganin abubuwa za su inganta idan basu farin ciki da yadda abubuwa ke gudana a yanzu. Sannu da kokari @ProfZulum."

Ga sauran sharhin a kasa:

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari za ta kafa masana'antun kera takalma da suturu na bilyoyin Naira a Kano da Aba

A wani labari na daban, hausawa mazauna jihar Cross Rivers sun yi wa ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo alƙawarin cewa za su mara wa yankin Kudu maso Gabas baya a yunkurin su na ganin shugaban Najeriya ya fito daga yankin a 2023.

Shugaban Hausawa da Fulani a jihar, Alhaji Salisu Abba Lawan ne ya bayyana hakan a yayin da mambobin Ohanaeze Ndigbo suka ziyarci fadarsa da ke Bogobiri a Calabar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel