Ba likitoci na tafi gani ba, hutu na tafi don in ga yara na, Gwamna Sule

Ba likitoci na tafi gani ba, hutu na tafi don in ga yara na, Gwamna Sule

- Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Abdullahi ya bayyana cewa ziyarar sa Amurka bata da alaka da duba lafiya

- Ya shaida cewa ya dauki hutun karshen shekara kamar yadda ya saba kuma ya tafi hutawa tare da iyalan sa a Houston da ke Texas

- Ya kuma kara da cewa yayi amfani da damar wajen yin gwajin lafiya kamar yadda ya saba tun kafin zaman sa gwamna amma lafiyar ƙalau

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya karyata jita jitar da ke cewa ya tafi Amurka ne don duba lafiyarsa, ya kuma bayyana cewa yaje Amurka don ziyartar yayan sa yayin da ya ke hutun karshen shekara.

Gwamnan ya yi ikirarin ne lokacin da ya bayyana a hirar gidan talabijin na Channels, kamar yadda kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Na tafi ziyarar yara na ne ba likitoci na tafi gani ba, Gwamna Sule
Na tafi ziyarar yara na ne ba likitoci na tafi gani ba, Gwamna Sule. Hoto: @LeadershipNGA
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe shugaban 'yan sintiri, sun sace mutane 8 a Katsina

Sule, wanda ake ganin ya wofantar da asibitocin jihar don tafiya duba lafiya zuwa Amurka, ya bayyana cewa yana daukar hutun shekara a watan Disamba kuma yayi amfani da wannan damar don ziyartar iyalan sa a Houston, Texas.

Gwamnan ya kara da cewa yayin da ya ke hutu a Amurka, inda ya dauki tsawon lokaci, ya yi amfani da damar don duba lafiyarsa.

KU KARANTA: Dan majalisa zai bawa 'yan mazabarsa tallafin zomo a matsayin jari (Hoto)

"Ziyara ta nan bata da alaka da lafiya. Nazo ne hutun karshen shekara. Kamar yadda na saba, ana duba lafiyata tun lokacin ina babban daraktan kamfanonin Dangote.

"Ba abin da ke damuna, lafiya ta ƙalau. Na kammala gwajin lafiya kamar yadda na saba, hakori, ido da komai kuma komai lafiya ƙalau," ya yi karin bayani.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel