Kimanin ma'aikatan lafiya 500 suka kamu da cutar Korona a Abuja, FCTA

Kimanin ma'aikatan lafiya 500 suka kamu da cutar Korona a Abuja, FCTA

- Ministan birnin tarayya ya bayyana adadin Likitoci, da sauran ma'aikatan asibitinta da Korona ta harba

- A jiya, mutane biyar kacal suka kamu da cutar a birnin tarayya Abuja.

Ma'aikatar kula da birnin tarayya Abuja (FCTA) ta ce Likitoci 476 ne suka kamu da cutar Korona tun lokacin bullarta a watan Febrairu, 2020 a Najeriya.

Anthony Ogunleye, Sakataren yada labaran Ministan FCT, Mohammed Musa Bello, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Talata a Abuja.

"Tun lokacin da aka samu bullar cutar COVID-19 a FCT, ma'aikatan lafiya 476, suka kamu da cutar. Wannan ya hada da Likitoci, ma'aikatan jinya, masu bada magani, masu gwaji, direbobi da dss," Ogunleye yace.

"Daga cikin wannan lamba, Likitoci 4 ne suka kamu. Na baya-bayan nan mace ce kuma ta mutu a asibitin Gwarimpa a makon. Ba'a sake samun ma'aikacin asibitin da ya kamu a mako daya ba yanzu," ya kara.

Ogunleye yace mutuwan ma'aikatan bai dakatar da wani aiki ba a asibitocin birnin tarayyar.

Ya bayyana hakan ne domin watsi da rahoton cewa Likitoci sun kauracewa aiki sakamakon mutuwan Likitoci 20.

KU KARANTA: Yan bindiga na kokarin shigowa Najeriya daga kasar Mali ta jihata, Gwamnan Oyo

Kimanin ma'aikatan lafiya 500 suka kamu da cutar Korona a Abuja, FCTA
Kimanin ma'aikatan lafiya 500 suka kamu da cutar Korona a Abuja, FCTA Hoto: @NCDCgov
Asali: Twitter

KU KARANTA: Daga yi mishi allurar rigakafin korona, tsoho mai shekaru 75 ya sheka lahira a Isra'ila

A bangare guda, mutane 397 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Litinin, 29 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 84,811 a Najeriya.

A jiya, mutane biyar kacal suka kamu da cutar a birnin tarayya Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng