Sarkin Hausawan Legas, HRH Alhaji Muhammadu Sani Kabir, ya rasu

Sarkin Hausawan Legas, HRH Alhaji Muhammadu Sani Kabir, ya rasu

- HRH Alhaji Muhammadu San Kabir, sarkin Hausawan jihar Legas ya rasu ranar Alhamis da ta gabata

- Marigayi Kabir ya taba zama mataimaki kafin daga bisani ya zama shugaban riko a karamar Mushin ta jihar

- Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya taya al'ummar mutanen arewa da ke zaune Legas alhinin rashin marigayi Kabir

Allah ya yi wa Sarkin Hausawan Legas, HRH Alhaji Muhammadu Sani Kabir, rasuwa yana da shekaru 57 a duniya.

A cikin wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya taya al'ummar mutanen arewa da ke zaune jiharsa alhinin mutuwar Sarkin.

Sanwo-Olu ya bayyana marigayi Kabir a matsayin dan gwagwarmaya wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaba kafin daga bisani ya zama shugaban riko a karamar Mushin.

KARANTA: Pantami Vs Dabiri, Malami Vs Magu da wasu sabani 3 da aka samu tsakanin hadiman Buhari

"Ya bayar da gudunmawa mai yawa domin ganin dorewar siyasa a Nigeria.

Sarkin Hausawan Legas, HRH Alhaji Muhammadu Sani Kabir, ya rasu
Sarkin Hausawan Legas, HRH Alhaji Muhammadu Sani Kabir, ya rasu
Asali: Twitter

"Ya na daga cikin 'yan gwagwarmaya da suka yi aiki da kungiyar NADECO domin yaki da soke zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993," a cewar Sanwo-Olu.

KARANTA: 'Yan sanda sun kama basarake da wata mata Sumayya saboda bawa 'yan bindiga mafaka da bayanai

Kazalika, Sanwo-Olu ya yi addu'ar Allah ya ji kansa.

Marigayi Kabir ya rasu ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Disamba, 2020, sannan an yi jana'izarsa tare binne gawarsa bisa tsarin addinin Musulunci a makabartar Musulmai ta Jafojo da ke yankin karamar hukumar Agege, jihar Legas.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa majalisar wakilan Najeriya ta fidda sanarwar ƙaryata neman afuwar Shugaba Buhari bisa gayyatarsa ya gurfana gaban majalisar don bayani kan matsalar tsaro da ta addabi ƙasa.

Sanarwar ta ƙaryata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai ke fitarwa kan cewar ƴan majalisar za su roƙi afuwar Shugaban ƙasa bayan sun amince da ƙudirin gayyatarsa, kamar yadda BBC ta wallafa.

Wasu ƴan majalisa daga jihar Borno ne suka nemi a gayyato shugaba Buhari don ya yi bayani akan halin rashin tsaro da ake fama da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng