Pantami Vs Dabiri, Malami Vs Magu da wasu sabani 3 da aka samu tsakanin hadiman Buhari
- Abubuwa da dama sun faru a gwamnatin Nigeria a cikin shekarar 2020 da muke bankwana da ita
- Wasu hadiman shugaban kasa sun shiga bakin manema labarai saboda sabani da rikicin da ya shiga tsakaninsu da juna
- Legit.ng Hausa ta fassara rahoton wasu daga cikin irin wadannan sabani da TheCable ta wallafa
1. Malami da Magu
Rigimar da ta ɓarke tsakanin dakataccen shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, da ministan shari'a, Abubakar Malami, ta samo asali ne daga zargin cin hanci da Malami ya yiwa Magu sannan ya ƙi yarda ya bayyana a ofishinsa.
Bayan da kwamitin da babban jojin kotun ɗaukaka ƙara ya kafa don bincikar Magu, malami ya buƙaci da a tsige Magu daga kujerar shugabancin hukumar EFCC.
Duk da kame Magu tare da tsare shi na tsawon kwanaki goma ana bincike, lauyansa ya zargi Malami da yi masa bita-da-ƙulli sannan ya kalubalance shi da fito da hujjojin laifin da ya ke zargin sa da aikatawa, lamarin da Malami har yanzu ya gaza bayyanawa.
2. Abike Dabiri da Pantami
Cikin watan Mayu ne Abike Dabiri-Erewa, shugabar hukumar NiDCOM, ta zargi ministan sadarwa Isa Pantami da tura yan bindiga da su kori ma'aikatan hukumar ta daga ofishin da hukumar sadarwa ta ba ta.
KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe shugaban PDP, Adamu Mohammed, sun yi awon gaba da 'ya'ayansa 'yammata uku
Pantami a martaninsa ya bayyana iƙirarin nata da ƙarya tsagoronta inda ya ce bai bayarda wani umarni ga wasu yan bindiga ba.
Sai dai Dabiri ta ce bai kamata a sami malamin addinin kamarsa ba da karya sannan da rashin girmama mace.
3. Ngige da NSITF
Ministan ƙwadago da ayyuka,Chris Ngige da Daraktan kula da inshorar Najeriya (NSITF) sun samu wani saɓani a tsakaninsu wanda ya yi sanadiyyar dakatar da wasu.
A wata wasiƙa mai kwanan watan 1 ga Yuli, 2020, wadda ta bayyana sahale dakatar da wasu ƙusoshin ma'aikatar NSITF da shugaban ƙasa yayi bisa zargin "rashin aiki dai dai da wasu laifuka da suke da alaƙa da cuwar cuwar kuɗaɗe".
KARANTA: Akwai maganar tsige Buhari a majalisa; dan majalisa ya tona asiri
An umarci wasu ƙusoshin hukumar da su miƙa ragamar kujeransu ga waɗanda suke biye musu a matsayi.
Sannan kuma su gurfana a gaban kwamitin da zai binciki harkar shiga da fitar da kudaden hukumar tun daga shekarar 2017 zuwa 2020.
Amma wasu ƙusoshi sun yi gardama inda su ka dawo ofisoshinsu, su na da'awar cewar Shugaban ƙasa bai bada wannan umarnin ba.
Ya ƙara da cewar matakin da Ministan ya ɗauka ya saɓawa umarnin Shugaba Buhari.
Sakataren gwamnatin tarayya bashida haƙƙin dakatarwa ko tsige shugaban wata hukuma ko ma'aikata da shugaban ƙasa ya naɗa.
Sai dai, bayan kwan gaba kwan baya tsakanin Ministan da Daraktan NSITF, wanda ya jawo taƙaddama tsakanin Chris Ngige da James Faleke, ɗan majalisa wanda ya yiwa ministan magana akan batun, wasu ƙusoshi sun bi sharuɗan dakatarwar.
4. Hukumar Aikin Ƴansanda da Babban Sufeton ƴan sanda
Ko waye yake da haƙƙin ɗaukar aiki a rundunar ƴan sandan Najeriya?
Wannan tambayar ita ce ta haddasa "rigima" tsakanin Hukumar Aikin ɗan sanda(PSC) da babban sufetan ƴansanda(IGP)Mohammed Adamu.
Bayan IGP ya ɗauki Kwansitabul 10,000 sai PSC ta garzaya gaban kotu tana ƙalubalantar matakin.
Wata babbar kotun tarayya ta yi watsi da ƙarar PSC a fari dalilin rashin hujja.
Sai dai kotun ɗaukaka ta sauya hukuncin inda ta rushe ɗaukar kwanstabul 10,000 da IGP ya ɗauka.
Amma, tuni IGP ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli ya na neman ta rusha hukuncin kotun baya.
Dukkan ɓangarori biyu (PSC da IGP) na jifan juna da zazzafan kalamai da martani da ke nuni da gazawar kowannensu.
5. KEYAMO vs DG NASIR LADAN
Wannan dambarwar ta fara ne tun daga lokacin da Shugaba Muhammad Buhari ya umarci Festus Keyamo, ministan ɗaukar aiki da ƙwadago, ya samar da ayyuka 774,000.
Ministan da kwamitin ɗaukar aiki da ƙwadago na majalisa sun fafata sakamakon yunƙurin ƴan majalisa "na yin uwa da makarɓiya akan batun" ɗaukar ayyukan.
Kwamitin majalisa ya ce kada Keyamo ya sake ya ja ragamar tsarin kuma tuni suka shirya maye gurbinsa da Nasir Ladan, daraktan hukumar ɗaukar ayyuka a ƙasa (NDE) don aiwatar da tsarin ɗaukar ƴan ƙasa 774,000 ayyuka.
Lokacin da ta bayyana a fili Darakta yana goyon bayan ƴan majalisa, Keyamo ya tura masa da takardar gargaɗi yana umartarsa da kada ya sake ya ɗauki wani mataki akan batun ɗaukar ayyukan ba tare da samun sahalewa a rubuce daga gare shi ba.
Ba'a yi mamaki ba da a ranar 8 ga watan Disamba aka kori Nasir Ladan kuma aka bawa Keyamo damar zaɓo sabon daraktan da zai maye gurbinsa.
Amma,majalisa ta yi kira ga shugaban ƙasa da ya sake duba, ya janye hukuncinsa na tsige Nasiru Ladan.
A ranar Juma'a ne Legit.ng ta rawaito cewa Allah ya yi wa majidadin Kano kuma makaman masarautar karaye, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, rasuwa.
Marigayi Musa Saleh ya kasance mahaifi wurin tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanata, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso
Za'a yi jana'izarsa da misalin karfe uku na ranar Juma'a a unguwar Bompai da ke cikin birnin Kano.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng