'Yan sanda sun kama basarake da wata mata Sumayya saboda bawa 'yan bindiga mafaka da bayanai

'Yan sanda sun kama basarake da wata mata Sumayya saboda bawa 'yan bindiga mafaka da bayanai

- Mai unguwar ƙauyen Tungan-Iliya da wasu mutane goma sun shiga hannu bisa zarginsu da kai hari a ƙaramar hukumar Mashegu dake jihar Neja

- Rundunar yan sanda ta ce ta na ƙara faɗaɗa bincikenta don ganin an kamo tare da gabatar da sauran masu laifin a gaban kotu domin yi musu hukuncin da ya dace

- Jihar Neja na fuskantar karuwar hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin baya bayan nan

Rundunar yan sanda ta jihar Niger, ta yi nasarar cafke mai unguwar ƙauyen Tungan-Iliya da wasu mutane goma bisa zarginsu da kai hari a ƙaramar hukumar Mashegu dake jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ne ya bayyana haka inda ya ce sun samu nasara ne biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu inda suka kai samame a maɓoyar maharan dake dajin Tunga-iliya.

Da ya ke zantawa da manema labarai Wasiu ya ce, "Dakarun mu sun yi musayar wuta da su inda aka kama bakwai cikin su, biyar kuma sun ji mummunan rauni.

"Cikin waɗanda ake zargi harda mai unguwar kauyen Tunga-iliya da Sumayya Bello wacce take kaiwa yan ta'addan bayanai."

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Arewa ta nemi a kama Kukah sannan a hukunta shi kan furucinsa game da Buhari

Mr Abiodun ya ce, rundunar yan sanda na ƙara faɗaɗa binciken ta don ganin an kamo tare da gabatar da su gaban kotu domin yi musu hukuncin da ya dace.

'Yan sanda sun kama basarake da wata mata Sumayya saboda bawa 'yan bindiga mafaka da bayanai
'Yan sanda sun kama basarake da wata mata Sumayya saboda bawa 'yan bindiga mafaka da bayanai
Asali: UGC

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun kashe wani mutum da aka bayyana sunansa da Ahmodu Mohammed, shugaban jam'iyyar PDP mazaɓar Kampala dake karamar hukumar Bosson jihar Niger.

Bugu da ƙari, bayan maharan sun kashe marigayin, ana kuma zargin sun sace yayan sa mata uku sun tafi da su kamar yadda rahoton jaridar TheCable ya bayyana.

A ranar Alhamis da ta gabata ne maharan, wadanda aka ce adadinsu ya haura mutum 15, suka kashe Mohammed bayan da suka kutsa kai cikin gidansa da misalin ƙarfe 2 na dare.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel