Majalisa ta musanta bawa Buhari hakuri, ta yi karin bayani

Majalisa ta musanta bawa Buhari hakuri, ta yi karin bayani

- An samu barkewar cece-kuce dangane da gayyatar da majalisar wakilai ta yi wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari

- Daga baya rahotanni sun bayyana cewa majalisa ta janye gayyatar tare da neman afuwar shugaba Buhari

- Sai dai, majalisar ta fito ta musanta hakan tare da yin karin bayani dangane da batun

Majalisar wakilan Najeriya ta fidda sanarwar ƙaryata neman afuwar Shugaba Muhammadu Buhari bisa gayyatarsa ya gurfana gaban majalisar don bayani kan matsalar tsaro da ta addabi ƙasa.

Sanarwar ta ƙaryata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai ke fitarwa kan cewar ƴan majalisar za su roƙi afuwar Shugaban ƙasa bayan sun amince da ƙudirin gayyatarsa, kamar yadda BBC ta wallafa.

Wasu ƴan majalisa daga jihar Borno ne suka nemi a gayyato shugaba Buhari don ya yi bayani akan halin rashin tsaro da ake fama da shi.

A sanarwar da ta fitar, majalisar ta bayyana labaran a matsayin na ƙanzon kurege.

KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su

Kakakin majalisar, Benjamin Kalu, shine ya fidda sanarwar.

Majalisa ta musanta bawa Buhari hakuri, ta yi karin bayani
Majalisa ta musanta bawa Buhari hakuri, ta yi karin bayani @Bashirahmad
Source: Twitter

Tun ranar 1 ga watan Disamba ne ƴan majalisar suka gayyaci Shugaba Buhari don ya yi musu bayani kan halin rashin tsaro da ƙasa ke ciki, amma sai ya yi burus da gayyatar duk da a farko ya nuna zai amsa gayyatar.

Ƴan majalisar jihar Borno sune suka buƙaci a sanya dokar ta ɓaci sannan a gayyato shugaban ƙasa don ya yi bayani kan yadda zai magance matsalar tsaro.

KARANTA: Akwai maganar tsige Buhari a majalisa; dan majalisa ya tona asiri

Kana kuma ya magantu kan yadda mayaƙan Boko Haram suka yiwa manoman shinkafa 43 "kisan kiyashi" ta hanyar yi musu yankan rago a Zabarmari, jihar Borno.

Da fari dai Shugaba Buhari ya amince da gayyatar, sai dai, daga baya Ministan Shari'a, Abubakar Malami, yace ƴan majalisa ba su da hurumin gayyato shugaban ƙasa ya gurfana gabansu.

Acewar Malami; bai dace Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya yi bayanan matsalar rashin tsaro a bayyane ba.

Ya ce su kansu ƴan majalisar na yin abubuwan da suka saɓawa doka da kundin tsarin mulkin Najeriya.

A cikin sanarwar Mr. Benjamin Kalu ya ce:

"Babu afuwar wanda majalisa ta nema, ta sauke nauyin aikin da ya rataya wuyanta ne kamar yadda tsariin mulkin ƙasa ya basu dama ƙarƙashin jagorancin Shugaban majalisa, Femi Gbajabiamila."

"Kuma ba ta yi wani da ya kauce ko saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasa ko ruguza dimokaraɗiyya ba."

A baya Legit.ng ta rawaito cewa mamba a majalisar wakilai kuma dan jam'iyyar PDP, Kingsley Chinda, zai fuskanci hukuncin ladabtarwa.

Honarabul Kingsley ya shiga tsaka mai wuya ne sakamakon kiran da ya yi na cewa a tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Dan majalisar ya ce shugaba Buhari ya gaza samar da tsaro a yankin arewa kuma ya ki amsa kiran majalisa domin yin jawabi a kan halin da tsaron kasa ke ciki

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel