Katsina: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 48, sun kashe 2
- Masu garkuwa sun sace a ƙalla mutane 48 daga ƙauyuka daban-daban a ƙaramar hukumar Batsari a Katsina
- Ƙauyukan da ƴan bindiga suka kai harin sun hada da Garin Dodo, Bakon Zabo, Biya-ka-Kwana, Tundun Modi da Watangadiya
- Wadanda suka sace sun hada da mata, maza har ma da wasu ma'aurata da aka sace kwana ɗaya bayan aurensu
A ƙalla mutane 48 ne ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Batsari bayan harin da suka kai a garuruwa huɗu.
Yasir Aminu, mazaunin Garin Dodo, ɗaya daga cikin garuruwan huɗu, ya ce ya yi tafiyan awa huɗu a kafa kafin ya kai Batsari bayan yan bindigan sun hari, HumAngle ta ruwaito.
"Sun kai hari ƙauyen mu cikin kwanaki biyu da suka gabata, sun sace fiye da mutum 30," in ji Aminu, ya cigaba da cewa, "mafi yawancin mutane sun gudu ba mu san inda suka tafi ba. Sun saba kawo mana hari kullum sai dai wannan ya yi muni".
DUBA WANNAN: Gwamnan Kano Ganduje ya yi wa Sanata Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifin sa
Mjiyar Legit.ng ta gano cewa ƴan bindigan sun saba kai hari ƙauyukan da ke wajen Batsari na tsawon watanni uku da suka gabata.
A cikin awa 48 da suka gabata, yan bindigan sun sace mutum 30 ciki har da maza da mata a Garin Dodo, yayin da sun sace mata 10 a ƙauyen Biya-Ka-Kwana a cewar majiyoyi daga ƙauyen.
"A kauyen Tudun Modi, an sace mutum uku yayinda an sace mutum biyar a ƙauyen Watangadiya," a cewar wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa.
"Yan bindiga sun cin karen su ba babaka a garuruwan domin an bar mutanen a hannun ƴan bindigan."
KU KARANTA: Sirrin cin galaba kan 'yan bindiga a Arewa yana Zamfara, in ji Matawalle
Kazalika, an sace wasu wani ango da amaryarsa a Bakon Zabo, wani ƙauye mai nisan kilomita 3 daga garin Batsari.
Yan bindigan sun sace amarya da ango kwana ɗaya bayan ɗaura aurensu," in ji Hassan Fari, wani shaidan gani da ido.
Ya ce har yanzu yan bindigan ba su tuntubi iyalan ba don neman kuɗin fansa kuma kawo yanzu hukumomin tsaro ba su riga sun ceto su ba.
A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.
Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.
Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng