Hotunan gwamnan APC sanye da kayan soja a cikin daji yana cin abinci tare da dakaru

Hotunan gwamnan APC sanye da kayan soja a cikin daji yana cin abinci tare da dakaru

- Ganin gwamnan Najeriya sanye da kayan sojoji abu ne da ba a cika gani ba a damokaradiyyar Najeriya

- Amma kuma, Gwamna Bello na jihar Kogi ya saka kayan sojoji inda ya shiga cikin dakarun da ke yakar rashin tsaro

- Gwamnan ya ziyarci sojojin da ke daji inda ya zauna suka ci abinci tare domin karfafa musu guiwa

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya nuna yadda yake da burin kawo karshen kalubalen da ke addabar arewa ta tsakiya a fannin tsaro.

A wasu hotunansa, an ga gwamnan jihar Kogin sanye da kayan sojoji inda ya tsinkayi dajin Irepeni da ke Kogi ta tsakiya domin ganawa da sojojin da ke dajin.

Wani Promise Emmanuel wanda ya bayyana kansa a matsayin babban sakataren yada labaran mataimakin gwamnan ya wallafa hotunan a Twitter a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba.

Hotunan gwamnan APC sanye da kayan soja a cikin daji yana cin abinci tare da dakaru
Hotunan gwamnan APC sanye da kayan soja a cikin daji yana cin abinci tare da dakaru. Hoto daga @KogiRebel
Source: Twitter

KU KARANTA: Rahoto: Yaran makarantan Kankara sun fallasa FG, sun bayyana hanyar da aka bi aka cece su

Mataimakin gwamnan jihar Kogi ya sake wallafa hotunan a shafinsa na Twitter, Legit.ng ta gano hakan.

Promise wanda ya bayyana cewa ziyarar gwamnan ya yi ta ne a watan Maris na 2018, ya kara da cewa gwamnan ya je duba yadda ayyukan sojojin suke gudana ne a Irepeni.

Ya ce gwamnan Kogi ya matukar jin dadin cin abinci a wuri daya tare da sojojin, alamun da ke nuna cewa yana tare da su dari bisa dari.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai wa dakarun soji hari, sun kashe sojojin ruwa 2

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana matukar shiga takaici da bakin ciki in har aka samu rashin zaman lafiya da karantsaye a kan tsaro a kasar nan.

Shugaban kasan a sakonsa na Kirsimeti ga 'yan Najeriya ya yi kira garesu da su bada goyon baya ga dakarun soji da sauran hukumomin tsaro.

"Da gangan ba zan ki sauke babban nauyin da ke kaina ba na tabbatar da tsaron rayuka da kadadrori ba. Ina shiga halin takaici matukar aka samu karantsaye a fannin tsaron kasar nan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel