Majalisar wakilai ta janye gayyatar Buhari, ta nemi afuwarsa
- Majalisar wakilai ta gayyaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, domin ya yi jawabi akan tabarbarewar tsaron kasa
- Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya amince zai amsa gayyatar majalisar
- Sai dai, daga baya, ministan shari'a, Abubabakar Malami (SAN), ya ce shugaba Buhari ba zai amsa gayyatar ba
Yan majalisar wakilai ta tarayya sun yi watsi da kudirinsu, a yanzu ko nan gaba, na yunkurin gayyatar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zauren Majalisar don ƙarin haske kan matsalar tsaro da ta dabaibaye yankin arewacin ƙasar nan.
A farkon watan da muke ciki ne wasu daga cikin yan majalisa suka gayyaci shugaban ƙasa domin jin yadda tsaro ke ƙara taɓarbarewa a yankin arewa biyo bayan yankan rago da kungiyar Boko Haram ta yiwa wasu manoma 43 a jihar Borno
Bayanai dake fitowa daga majalisar na nuna cewa, majalisar ta yi watsi da batun kara gayyatar shugaban kasar a yanzu ko nan gaba don yin bayani kan sha'anin tsaro.
KARANTA: Akwai maganar tsige Buhari a majalisa; dan majalisa ya tona asiri
Wasu 'yan majalisar sun bayyana cewa, kiran na da alaƙa da siyasa domin cin zarafin shugaban kasa, kamar yadda rahoton TheCable ya bayyana.
"Mun fahimci cewa yan majalisar ma da suka ɗau nauyin kudirin sun bi ta bayan fage sun nemi afuwar fadar shugaban ƙasa kan dagewa lallai sai ya amsa gayyatar."
KARANTA: Dan majalisa ya kira taron manema labarai, ya sanar da sakin matarsa saboda ta sauya jam'iyya
Ya kara da cewa gayyatar ta kawo rabuwar kai har ake mata kallon "...ta juye, yanzu sha'anin ya rikide zuwa bangaranci tsakanain yankin kudu da arewa saboda saɓanin siyasa da ke gida."
Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa shugaba Buhari zai amsa gayyatar majalisar kafin daga bisani ministan shari'a, Abubakar Malami, ya sanar da cewa shugaban kasar ba zai amsa gayyatar ba.
A baya Legit.ng a rawaito cewa wani mamba a majalisar wakilai ta tarayya na gab da shiga tsaka mai wuya sakamakon kiran da ya yiwa majalisar da ta tsige shugaban ƙasa bisa gazawa wajen samar da tsaro a Najeriya.
Dan majalisar wakilan, Kingsley Chinda, mai wakiltar Obia/Akpor kuma ɗan jam'iyyar PDP, ya bukaci da a tsige shugaba Muhammadu Buhari ranar 7 ga Disamba biyo bayan yankan rago da yan kungiyar Boko Haram ta yiwa wasu manoma a Zabarmari.
Kazalika, ya ce bai kamata a bar batun kin bayyanar da shugaban kasar ya yi a zauren Majalisar don karin bayani kan taɓarbarewa tsaro ta wuce haka ba.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng