Dan majalisa ya kira taron manema labarai, ya sanar da sakin matarsa saboda ta sauya jam'iyya

Dan majalisa ya kira taron manema labarai, ya sanar da sakin matarsa saboda ta sauya jam'iyya

- Dan majalisar dokoki, Sumitra Khan, ya kira taron manema labarai tare da sanar da sakin matarsa

- Sumitra ya sanar da sakin matarsa, Sujata Mondal, jim kadan bayan ta sanar da cewa ta bar jam'iyyarsa a taron manema labarai

- Sumitra, cikin hawayen takaici, ya zargi jam'iyyar adawa da rusa masa gida ta hanyar sace masa matarsa, farin cikinsa

Dan majalisar dokoki a kasar India ya sawwakewa matarsa, da suka shafe shekaru goma tare, saboda ta sauya jam'iyya, kamar yadda BBC ta rawaito.

Sumitra Khan, mamba a jam'iyyar BJP ta firaminista Narendra Modi, ya aikawa matarsa, Sujata Mondal Khan, takardar saki bayan ta koma jam'iyyar TMC.

Sumitra da Mondal sun fito ne daga jihar Bengal da ke yammacin kasar India, inda kuma ake Shirin fafatawa a tsakanin BJP da TMC a zaben kujerar majalisar dokoki.

A ranar Litinin ne uwargida Mondal ta sanar da cewa ta sauya sheka zuwa jam'iyyar TMC yayin wani taro da manema labarai a Kolkata, babban birnin jihar Bengal.

KARANTA: Kage da kazafi: IGP Adamu ya shigar da karar dan takarar shugaban kasa a 2019

Jim kadan bayan uwargida Mondal ta sanar da hakan, dan majalisa Sumitra ya kira wani taron manema labarai cikin gaggawa.

Dan majalisa ya kira taron manema labarai, ya sanar da sakin matarsa saboda ta sauya jam'iyya
Dan majalisa ya kira taron manema labarai, ya sanar da sakin matarsa saboda ta sauya jam'iyya @BBC
Asali: Twitter

Cikin hawaye da takaici, Sumitra ya sanar da cewa ya sawwake wa matarsa, ya rabu da ita, duk da sun rayu na tsawon shekaru goma, saboda ta sauya sheka.

KARANTA: An kama 'Ahmed Musa' na bogi da laifin damfarar N700,000 a Kano

Dan majalisar ya sanar da cewa daga yanzu Mondal ta na da 'yanci, ya sakar mata mara, ta je ta cimma dukkan burikanta na siyasa amma ta cire sunansa daga jikin sunanta.

Kazalika, ya zargi jam'iyyar TMC da lalata masa gida ta hanyar kwace masa matarsa, farin cikinsa, da suka sha soyayya ta tsawon lokaci.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce sun bankado wata makarkashiya mai kama da juyin mulki da ake shiryawa shugaba Buhari.

A cewar Adesina, masu shirya wannan makarkashiya na shirin fara yada wasu labaran karya a 'yan kwanaki masu zuwa.

Adesina ya ja hankalin 'yan Nigeria su yi watsi da duk wata jita-jita da karya da za'a yada nan da wani takaitaccen lokaci mai zuwa a gaba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel