Miyagu sun halaka mutum 7, sun kone mota dankare da buhunan masara a Kaduna

Miyagu sun halaka mutum 7, sun kone mota dankare da buhunan masara a Kaduna

- Mutum bakwai ne suka rasa rayukansu wadanda suka hada da 'yan sa kai 2 a Galadimawa

- Miyagun 'yan bindiga sun kai hari kasuwar mako ta Galadimawa da ke Giwa jihar Kaduna

- Babu kakkautawa jami'an tsaro suka bi su inda suka ragargaza wasu yayin da wasu suka tsere

A kalla mutum bakwai da suka hada da 'yan sa kai biyu suka mutu bayan 'yan bindiga sun bude musu wuta a kasuwar mako ta Galadimawa da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Samuel Aruwan, kwamishinan cikin gida ya sanar a ranar Alhamis, 'yan ta'addan sun shiga kasuwar wurin karfe 4 na yammacin ranar Laraba kuma suka bude wa jama'a wuta.

Aruwan ya bada sunayen wadanda aka kashe kamar haka: Yusuf Magaji Iyatawa, Dabo Bafillace, Danjuma Haladu, Shuaibu Isyaku, Isyaku Adamu, Shehu Dalhatu da Musa Haruna Kerawa.

KU KARANTA: Da duminsa: Dalibai za su yi gagarumar zanga-zanga matukar ASUU suka koma yajin aiki, NANS

Miyagu sun halaka mutum 7, sun kone mota dankare da buhunan masara a Kaduna
Miyagu sun halaka mutum 7, sun kone mota dankare da buhunan masara a Kaduna. Hoto daga @HumAngle
Asali: Twitter

Ya kara da cewa wani direba mai suna Yusuf Tumburku wanda ya gama yin lodi ya fuskanci ibtila'i domin kuwa miyagun sun banka wa motar wuta.

Akwai wata mota da miyagun suka banka wa wuta, Aruwan yace.

Kwamishinan ya kara da bayyana cewa hukumomin tsaro da suka hada da 'yan sanda tare da sojoji sun banki miyagun inda suka tsere.

Ya ce 'yan bindiga da suka isa wurin suna kan babura a kalla 15 kuma jami'an tsaron sun yi nasarar halaka wasu daga ciki

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya mika ta'aziyyarsa ga iayalan wadanda suka rasa rayukansu.

KU KARANTA: Hotunan ango Sulaiman Panshekara ya daga Amurka da dattijuwar baturiyar matarsa

A wani labari na daban, daga bakin wasu daga cikin yaran makarantar Kankara da aka sace, sun tabbatar da cewa an biya kudin fansa kafin a sakesu, mujallar The Wall Stree ta tabbatar.

Akasin ikirarin gwamnatin tarayya da cewa babu sisin kwabo da aka biya domin kubutar da dalibai 334 daga hannun 'yan bindiga.

A wani rahoton ranar Laraba, WSJ ta ce uku daga cikin daliban da aka sace sun tabbatar da cewa an biya kudi kafin a sakesu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel