Rahoto: Yaran makarantan Kankara sun fallasa FG, sun bayyana hanyar da aka bi aka cece su

Rahoto: Yaran makarantan Kankara sun fallasa FG, sun bayyana hanyar da aka bi aka cece su

- Daliban GSSS Kankara sun bayyana cewa kudin fansa aka biya sannan aka cece su

- Daliban sun sanar da cewa, a kalla an biya miliyan 1 a kan kowanne dalibin da aka sace

- Amma gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu sisin kwabo da ta biya don fansar su

Daga bakin wasu daga cikin yaran makarantar Kankara da aka sace, sun tabbatar da cewa an biya kudin fansa kafin a sakesu, mujallar The Wall Stree ta tabbatar.

Akasin ikirarin gwamnatin tarayya da cewa babu sisin kwabo da aka biya domin kubutar da dalibai 334 daga hannun 'yan bindiga.

A wani rahoton ranar Laraba, WSJ ta ce uku daga cikin daliban da aka sace sun tabbatar da cewa an biya kudi kafin a sakesu.

Ta kara da cewa, wani da ya san abinda ya wakana tsakanin masu garkuwa da mutanen da gwamnati, ya ce an biya wasu manyan kudade kashi daban-daban ga masu garkuwa da mutanen.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Ba zan taba neman sasanci ko ciniki da 'yan bindiga ba, Yahaya Bello

Rahoto: Yaran makarantan Kankara suna fallasa FG, sun bayyana hanyar da aka bi aka cece su
Rahoto: Yaran makarantan Kankara suna fallasa FG, sun bayyana hanyar da aka bi aka cece su. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

A ranar Juma'a, 11 ga watan Disamban 2020 wasu 'yan bindiga suka kwashe daliban makarantar gwamnati ta kimiyya da ke Kankara.

Bayan ceto daliban a ranar 17 ga watan Disamban 2020, Garba Shehu hadimin shugaban kasa ya ce ceto yaran ya samu jagorancin tubabbun 'yan bindiga ne.

Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara ya ce shi ya tabbatar da ceto yaran ta hannun kungiyar Miyetti Allah da tubabbun 'yan bindiga.

WSJ ta ruwaito yadda daya daga cikin yaran ya bayyana cewa an tirsasa su cin danyen dankali da ganyen kalgo domin su rayu.

"Sun yi barazanar sakin 30 daga cikinmu bayan da aka biya su miliyan 30," rahoton yace daga bakin Yunusa Idris mai shekaru 16.

“Sun kwashi 30 daga cikinmu a babura da niyyar sakinmu."

Imran Yakubu, dalibi mai shekaru 17 ya ce kowanne daga cikinsu sai da aka biya mishi miliyan daya a yayin da suke barazanar kashe su ko su mayar da su cikinsu.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon dan Najeriya sanye da babban riga ana rantsar da shi a Amurka bayan ya lashe zabe

A wani labari na daban, wani Mustapha daga Kaduna ya ce Allah na bai wa matan aure lada sakamakon ayyukan gidansu da suke yi. Ayyukan sun hada da share-share, girki da kuma kula da gida ballantana idan aka yi domin farantawa maigida rai.

"Kwatanta irin ladar da mutum ke samu daga Allah idan kika yi ayyukan gida kamar su girki, tsaftace gida da kuma kula da shi.

"Lada ce a akan lada. Matan da basu yi aure ba sun rasa wannan ladan tare da matan auren da suka zabi barin wadannan ayyukan," Mustapha ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel