Da duminsa: Dalibai za su yi gagarumar zanga-zanga matukar ASUU suka koma yajin aiki, NANS

Da duminsa: Dalibai za su yi gagarumar zanga-zanga matukar ASUU suka koma yajin aiki, NANS

- Kungiyar daliban Najeriya ta tabbatar da cewa za ta fada gagarumar zanga-zanga idan ASUU ta koma yajin aiki

- Kungaiyar ta ce abun kunya ne da takaici yadda kungiyar tace ta janye yajin aikinta amma da sharadi

- Matukar kuwa kungiyar ta koma yajin aiki, daliban Najeriya za su fita kwan su da kwarkwata domin zanga-zanga

Kungiyar daliban Najeriya ta ce mambobinta za su shiga gagarumar zanga-zanga idan har kungiyar malamai masu koyarwa a jami'o'i suka sake fadawa yajin aikin.

Shugaban NANS, Sunday Asefon, ya sanar da hakan a wata tattaunawa da jaridar The Punch a ranar Alhamis.

Ya ce abun kunya ne da takaici yadda ASUU take sake barazanar sabon yajin aiki bayan bata wa daliban Najeriya watanni tara a banza.

KARANTA: Rashin tsaro: Ba zan taba neman sasanci ko ciniki da 'yan bindiga ba, Yahaya Bello

Da duminsa: Dalibai za su yi gagarumar zanga-zanga matukar ASUU suka koma yajin aiki, NANS
Da duminsa: Dalibai za su yi gagarumar zanga-zanga matukar ASUU suka koma yajin aiki, NANS. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Facebook

Asefon ya ce, "Wannan abun kunya ne a garemu da ASUU tace ta janye yajin aiki amma da sharadi. Idan suka koma aiki da sharadi, mu ma za mu tsaya da shirin mu na fara zanga-zanga.

"Amma idan suka koma yajin aiki, za mu hau tituna tunda yaren da kadai suke ganewa kenan, shi za mu yi musu."

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi, a ranar Laraba a Abuja ya sanar da janye yajin aikin da aka kwashe watannin tara ana yi amma da sharadi.

Ogunyemi wanda yace an janye yajin aikin a ranar Alhamis, 24 ga watan Disamban 2020, ya tabbatar da cewa kungiyar za ta sake komawa yajin aikin matuukar gwamnati ta kasa cika alkawarinta.

KU KARANTA: Tsaro: Reno Omokri ya sha alwashin bai wa Garba Shehu $20,000 in ya kwana a Koshebe ko Kware

A wani labari na daban, kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i (ASUU) a ranar Talata, 22 ga watan Disamban 2020, ta bada satar amsa a kan lokacin da za ta kawo karshen yajin aikinta na watanni 9.

Kungiyar ta sanar da hakan a wata wallafa da tayi a shafinta na Twitter.

Kamar yadda wallafa ta ce: "Labari mai dadi. Za a janye yajin aiki idan har gwamnatin tarayya ta biya dukkan albashin da malamai ke bin ta."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel