COVID-19 ta sa an soke ziyartar Fadar Shugaban kasa a lokacin bikin Kirismeti

COVID-19 ta sa an soke ziyartar Fadar Shugaban kasa a lokacin bikin Kirismeti

-Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kashe ziyarar kirismeti a 2020

-Garba Shehu ya bayyana wannan matakin da shugaban kasar ya dauka

-Buhari ya hana a kawo masa ziyara ne domin hana yaduwar COVID-19

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana matakin da ya dauka game da kawo masa ziyarar kirismeti a lokacin da ake fama da annobar COVID-19.

Shugaban Najeriyar ya bayyana cewa a wannan shekarar ba zai karbi ziyarar da aka saba kawowa fadar shugaban kasar a irin wannan lokaci ba.

Mai girma Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi ta bakin Hadiminsa, Garba Shehu, ya ce ya soke duk wata ziyarar kirismeti da ake shirin kawo masa yau.

A cewar shugaban kasar, wannan ya na cikin sharuda da dokokin da kwamitin PTF mai yaki da annobar COVID-19 ya gindiya domin rage yaduwar cutar.

KU KARANTA: Garba Shehu ya fallasa Reno Omokri, ya ce ‘Ka rike dalolinka, ba na bukata'

COVID-19 ta sa an soke ziyartar Fadar Shugaban kasa a lokacin bikin Kirismeti
PTF ta ziyarci Buhari a Fadar Shugaban kasa Hoto: Twitter / @MBuhari
Source: Twitter

A jawabinsa, shugaban kasar ya ba mutanen Najeriya su zama masu bin dokar da aka kafa domin ganin an takaita yaduwar kwayar wannan mummunan ciwo.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar da wannan jawabi ne a ranar jajibirin bikin kirismeti, Alhamis, 24 ga watan Disamba, 2020.

“Shugaban kasa ya yi kira ga duka mutane su bi sharudan da aka gindaya, su rika bada tazara, a rika amfani da takunkumi, a wanke hannu, a guji shiga cinkoso.”

Muhammadu Buhari ya ja-kunnen jama’a su kauracewa cincirindo a kasuwanni da wuraren ibadu.

KU KARANTA: COVID-19: Za a rika bude wuraren a ranakun Juma’a da Lahadi a Ekiti

Shugaba Buhari ya kuma yi kira ga al’umma su dakatar da duk wata tafiyar da ba ta zama dole ba a irin wannan yanayi, Shehu ya fitar da wannan jawabi a Twitter.

Ana rade-radin cewa mutanen Najeriya sun soma kamuwa da Coronavirus da ba a gama gane kanta ba bayan wani irin nau'in cutar ya bayyana a kasar Ingila.

Wasu masana da ke aiki a cibiyar bincike a Osun, su na ikirarin akwai sabuwar samfurin Coronavirus da ta rikida a Ingila da ta shiga jikin wasu mutanen.

Hukumomi suna binciken ko sabuwar COVID-19 mai mummunan hadari ta shigo daga ketare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel