Hotunan ango Sulaiman Panshekara ya daga Amurka da dattijuwar baturiyar matarsa

Hotunan ango Sulaiman Panshekara ya daga Amurka da dattijuwar baturiyar matarsa

- Saurayin ango, Sulaiman Panshekara ya daga kasar Amurka tare da baturiyar matarsa

- Matashin dan asalin jihar Kano ya auri masoyiyarsa, dattijuwar baturiya da suka hadu a Instagram

- Bayan daura aurensu a Najeriya, sun yi auren kotu sannan ta dauka mijinta suka kama hanyar Amurka

Ango Sulaiman Isah Panshekara ya daga zuwa kasar Amurka tare da dattijuwar baturiyar matarsa.

Idan za mu tuna, an daura auren dattijuwar baturiya da ta biyo saurayi Sulaiman Isah Panshekara har garin Kano.

Wannan lamarin ya janyo cece-kuce tun daga farkon zuwanta garin Kano kafin a saka kullen korona.

Hotunan ango Sulaiman Panshekara ya daga Amurka da dattijuwar baturiyar matarsa
Hotunan ango Sulaiman Panshekara ya daga Amurka da dattijuwar baturiyar matarsa. Hoto daga @Abdulhamied AA
Source: Twitter

KU KARANTA: Tsaro: Reno Omokri ya sha alwashin bai wa Garba Shehu $20,000 in ya kwana a Koshebe ko Kware

Hotunan ango Sulaiman Panshekara ya daga Amurka da dattijuwar baturiyar matarsa
Hotunan ango Sulaiman Panshekara ya daga Amurka da dattijuwar baturiyar matarsa. Hoto daga @Abdulhamied AA
Source: Twitter

Jama'a da dama sun dinga sukar wannan hadin ganin cewa Sulaiman matashi ne mai shekaru 23 yayin da dattijuwar baturiyar ke da shekaru 46 a duniya.

Sun dai daga zuwa kasar Amurka bayan da aka gama shagalin aurensu na gargajiya tare da yin auren kotu a kasar Najeriya.

Hotunan ango Sulaiman Panshekara ya daga Amurka da dattijuwar baturiyar matarsa
Hotunan ango Sulaiman Panshekara ya daga Amurka da dattijuwar baturiyar matarsa. Hoto daga @Abdulhamied AA
Source: Twitter

KU KARANTA: Ke kadai kika yi dawainiyata har na kawo haka, mai bautar kasa tana jinjinawa mahaifiyarta (Bidiyo)

A wani labari na daban, a yayin da cutar korona ke cigaba da barkewa a karo na biyu, lamuran 'yan bindiga tare da sauran laifuka suna kara kamari a arewa, jaridar Vanguard ta wallafa hakan.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya bello ya jaddada cewa ba zai taba sasanci ko ciniki da 'yan ta'adda ba, cewa 'yan ta'addan na amfani da wannan sassaucin wurin haukata gwamnati tare da ganin gazawarta.

Bello ya sanar da hakan ne a ranar Laraba a Abuja yayin wani shirin safiya a gidan talabijin wanda Vanguard ta kula da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel