Barkowar COVID-19 gadan-gadan ta sa Gwamnatin Ekiti ta gindaya sababbin sharuda

Barkowar COVID-19 gadan-gadan ta sa Gwamnatin Ekiti ta gindaya sababbin sharuda

- Gwamnatin Ekiti ta kawo sababbin dokoki a dalilin dawowar Coronavirus

- Kayode Fayemi ya ce sau daya za a koma bude wuraren ibada cikin mako

- An yafewa duk Jami’an Gwamnati da ba su kai mataki na 12 ba zuwa ofis

Gwamnatin jihar Ekiti ta sake garkama sabon takunkumi domin kare lafiyar al’umma, a sakamakon cutar COVID-19 da ta sake dawo wa da karfinta.

Jaridar Punch ta ce daga cikin matakan da gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi ya dauka, har da rufe makarantu da kuma takaita bude dakunan ibada.

Gwamnati ta umarci shugabannin addinai su rika bude wuraren ibadunsu sau daya a mako, sannan a rage adadin wadanda su ke zuwa wajen ibada da 50%.

Mai girma gwamna Kayode Fayemi na Ekiti ya ambaci wadannan sharuda da ya kawo domin yaki da cutar Coronavirus da ta sake dawowa a karo na biyu.

KU KARANTA: Ba za mu rufe Filato ba - Gwamna Lalong

Da yake jawabi, gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki ya zama dole domin ganin cewa annobar COVID-19 ba tayi barkewar da za ta yi kamari ba.

A jawabin na sa na ranar Laraba, 23 ga watan Disamba, 2020, gwamna Fayemi ya ce makarantu za su cigaba da kasancewa a rufe har 18 ga watan Junairu.

Bayan haka gwamnati ta haramta kwana ana ibada, da kuma rawa da cashewa a gidajen disko.

Gwamnan ya ce daga yanzu manyan jami’an gwamnati da su ka haura mataki na 12 a wajen aiki kadai ne aka halattawa fita daga gida su tafi wurin aikinsu.

KU KARANTA: COVID-19 ta sa abin da Kano za ta kashe a 2021 ya ragu

Barkowar COVID-19 gadan-gadan ta sa Gwamnatin Ekiti ta gindaya sababbin sharuda
Gwamnnan Ekiti Fayemi Hoto; twitter.com/kfayemi?
Asali: Twitter

Idan za ayi wani taro, gwamnati ta bada umarni a bi dokoki, a rage rabin adadin mutanen da ya kamata su hallara, sannan ba za a zarce karfe 8:00 na dare ba.

Fayemi ya ce ka da a cika sosai wajen birne gawa a makabartu, sannan ya bukaci otel da gidajen biki su bi dokokin da aka sani na hana yaduwar wannan cuta.

Kun ji cewa Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehanire, ya fadawa 'yan majalisa cewa gwamnatin tarayya na bukatar N400bn domin sayen maganin COVID-19.

Ministan ya shaidawa majalisar dattawa ana bukatar wadannan kudi domin sayawa mutanen Najeriya rigakafin cutar Coronavirus da ta ke kashe Bayin Allah.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng