Rashin tsaro: Ba zan taba neman sasanci ko ciniki da 'yan bindiga ba, Yahaya Bello
- Miyagun al'amura da 'yan ta'adda suna cin karensu babu babbaka duk da yaduwar cutar korona
- Gwamna Yahaya Bello ya jaddada cewa babu sasanci ko ciniki tsakaninsa da 'yan ta'adda
- Ya sanar da cewa hakkin samar da tsaro hakki ne da ya hau kowa ba sai jami'an tsaro ba
A yayin da cutar korona ke cigaba da barkewa a karo na biyu, lamuran 'yan bindiga tare da sauran laifuka suna kara kamari a arewa, jaridar Vanguard ta wallafa hakan.
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya bello ya jaddada cewa ba zai taba sasanci ko ciniki da 'yan ta'adda ba, cewa 'yan ta'addan na amfani da wannan sassaucin wurin haukata gwamnati tare da ganin gazawarta.
Bello ya sanar da hakan ne a ranar Laraba a Abuja yayin wani shirin safiya a gidan talabijin wanda Vanguard ta kula da shi.
KU KARANTA: Ke kadai kika yi dawainiyata har na kawo haka, mai bautar kasa tana jinjinawa mahaifiyarta (Bidiyo)
Gwamnan ya doka misali da kungiyar masu laifin da aka yi wa rangwame a jihar Nasarawa bayan shigar wani babban dan siyasa lamarin.
Ya jajanta cewa hakan yasa kungiyar ta cigaba da miyagun laifukanta. Ya kara da cewa burin siyasa babba zai iya zama silar tabbatar da tsaro a kasar nan.
Gwamnan ya kara da cewa tabbatar da tsaro ba wai hakkin dakarun sojin kasar nan bane, 'yan sanda ko sauran jami'an tsaro.
Hakki ne na kowa da kowa kuma ya zamana dole jama'a su samar da bayanan sirri a matsayin gudumawarsu.
KU KARANTA: Da duminsa: Kotun shari'a ta bada umarnin damko mawakin Buhari, Dauda Kahutu Rarara
A wani labari na daban, Ofishin Antoni janar na tarayya sun kasa martani a kan halin da ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar Zamani na Facebook, Mubarak Bala yake ciki.
Wata kotun tarayya da ke zama a Abuja ta bada umarnin sakin Mubarak Bala bayan watannin da ya kwashe a tsare.
Sakon da aka aike wa antoni janar na tarayya bai samu martani ba har a lokacin rubuta wannan rahoton.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng