Bawan Allah ya bayyanawa mata falalar da ke tattare da ayyukan cikin gida

Bawan Allah ya bayyanawa mata falalar da ke tattare da ayyukan cikin gida

- Wani bawan Allah mai suna Mustapha ya nusar da mata falalar da ke cike da ayyukan gida

- Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter, akwai matukar lada ga mace mai ayyukanta da kanta

- Amma kuma tabbas babu wata azaba ko ladabtarwa daga Allah ga wacce tace ba za ta yi ba

Wani Mustapha daga Kaduna ya ce Allah na bai wa matan aure lada sakamakon ayyukan gidansu da suke yi.

Ayyukan sun hada da share-share, girki da kuma kula da gida ballantana idan aka yi domin farantawa maigida rai.

"Kwatanta irin ladar da mutum ke samu daga Allah idan kika yi ayyukan gida kamar su girki, tsaftace gida da kuma kula da shi.

"Lada ce a akan lada. Matan da basu yi aure ba sun rasa wannan ladan tare da matan auren da suka zabi barin wadannan ayyukan," Mustapha ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Talata.

KU KARANTA: Ke kadai kika yi dawainiyata har na kawo haka, mai bautar kasa tana jinjinawa mahaifiyarta (Bidiyo)

Bawan Allah ya bayyanawa mata falalar da ke tattare da ayyukan cikin gida
Bawan Allah ya bayyanawa mata falalar da ke tattare da ayyukan cikin gida. Hoto daga @Aadam_Mustapha
Source: Twitter

Ya tabbatar da cewa babu wani azaba ga matan da suka zabi rashin yin ayyukan amma kuma akwai lada mai yawa ga wadanda suka yi.

KU KARANTA: Batanci ga Annabi: FG ta yi shiru a kan umarnin kotu na sakin Mubarak Bala

A wani labari na daban, wata matar aure ta wallafa labarinta mai cike da taba zuciya. Ta bada labarain yadda 'yar uwarta makusanciya ta koma kishiyarta dare daya.

A kokarinta na bai wa wata kwarin guiwar shawo kan matsalar aurenta, ta bada labarin yadda ta yi haihuwa ta biyu amma saboda rashin uwa, sai 'yar uwarta ta je mata zaman jego.

Kamar yadda ta bayyana, bayan isowar 'yar uwarta, sai ta fara wata boyayyar alaka da mijinta. Babu dadewa kuwa 'yar uwarta ta samu juna biyu kuma mijin ta ne ya dirka mata, The Nation ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel