An kama 'Ahmed Musa' na bogi da laifin damfarar N700,000 a Kano

An kama 'Ahmed Musa' na bogi da laifin damfarar N700,000 a Kano

- Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kano sun kama wani matashi, Gambo Yakubu, bisa zarginsa da sojan gona da damfara

- Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce mutumin ya damfari mutane 15 sama da Naira dubu dari bakwai

- An gano cewa matashin ya dauki budurwarsa tare da tafiya wani Otal a Sabon Gari inda suka kashe kudin jama'ar da ya damfara

Hukumar yan sandan Nigeria reshen jihar Kano ta tabbatar da kame wani mutum dan shekara 30 bisa laifin damfarar mutane sama da Naira 700,000

Mutumin, mai suna Gambo Yakubu, an kama shi ne bayan ya damfari mutane kudi sama da N700,000 ta hanyar amfani da sunan babban kaftin din kungiyar kafa ta Najeriya, super Eagles, wato Ahmad Musa.

An kama 'Ahmed Musa' na bogi da laifin damfarar N700,000 a Kano
An kama 'Ahmed Musa' na bogi da laifin damfarar N700,000 a Kano. Hoto: @AhmedMusa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu garkuwa sun kai hari Kano, sace dan kasuwa sun kuma kone motar 'yan sanda

Mutumin na fakewa da sunan zai taimakawa mutane domin su samu damar kwantiragi da kungiyoyin ƙwallon ƙafa dake Turai, inda ya ke neman su kawo kuɗi domin samun wannan damar.

Biyo bayan kama shi ɗin ne, sai aka same shi da takardu dake ɗauke da sunan shahararren ɗan ƙwallon ƙafar nan Ahmad Musa, wanda ya ke amfani da su don samun biyan buƙatar sa.

Jaridar Premium Times ta ce, "Ana zaton ya damfari mutane sama da 15 ta wannan hanyar wanda adadin kuɗin su ya haura N700,000 daga bisani kuma ya kashewa budurwarsa kuɗaɗen a wani hotel da suke zama cikin Sabon Garin Kano."

KU KARANTA: Adama Indimi ta taya mijinta murnar zagayowar ranar haihuwarsa da kamalai masu ratsa zuciya (Hotuna)

A ta bakin wanda ake zargi, Yakubu ya ce, "Ya na sayar da fom kan kudi N5000 matasa da suke tsananin buƙatar buga ƙwallo a ƙasashen waje."

DSP Abdullahi Haruna, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, ya tabbatar da kama matashin wanda shima ya taɓa bugawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Super Eagles.

A wani rahoton daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce duba da girman iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar, Allah ne kadai zai iya tsare iyakokin yadda ya kamata, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da ya ke jawabi yayin karbar bakuncin tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, wadda ke jagorancin tawagar sa ido kan zabe ta ECOWAS a Nijar, Buhari ya ce zai iya duk mai yiwuwa don kawo zaman lafiya a yankin na Sahel.

A cewar sanarwar da Femi Adesina, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan labarai, shugaban kasar ya jinjinawa takwararsa na Nijar, Shugaba Muhamadou Issoufou, "don bai yi yunkurin sauya kundin tsarin mulki ba don zarcewa bayan kure wa'adinsa biyu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel