Fadar shugaban kasa: Ana shiryawa Buhari wata makarkashiya mai kama da juyin mulki

Fadar shugaban kasa: Ana shiryawa Buhari wata makarkashiya mai kama da juyin mulki

- Femi Adesina, mai magana da yawuun shugaban kasa, ya ce sun bankado wata makarkashiya da ake shiryawa shugaba Buhari

- A cewar Adesina, masu shirya wannan makarkashiya na shirin fara yada wasu labaran karya a 'yan kwanaki masu zuwa

- Adesina ya ja hankalin 'yan Nigeria su yi watsi da duk wata jita-jita da karya da za'a yada nan da wani takaitaccen lokaci mai zuwa a gaba

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Femi Adeshina, ya bayyana cewa akwai wata makarkashiya mai kama da juyin mulki da ake shiryawa shugaban ƙasa da cewa wai ba shi ne ke mulkin ƙasar nan ba.

Cikin bayanan nasa, Adeshina ya ce masu kulla wannan makarkashiya na shirin yaɗa wasu labaran ƙarya nan da yan kwanaki masu zuwa, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Ya ja hankalin jama'a da su yi watsi da da duk jita-jita da za su kitsa don bata shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

KARANTA: Kage da kazafi: IGP Adamu ya shigar da karar dan takarar shugaban kasa a 2019

Fadar shugaban kasa: Ana shiryawa Buhari wata makarkashiya mai kama da juyin mulki
Fadar shugaban kasa: Ana shiryawa Buhari wata makarkashiya mai kama da juyin mulki @Channels
Asali: Twitter

"Muna janyo hankalin jama'a da su zama cikin shirin ganin wani gangami domin bata shugaban ƙasa da ofishinsa domin cimma wani buri na siyasa da ake kitsawa ta yanar gizo" Kamar yadda mai magana da yawun shugaban ƙasa Femi Adeshina ya ce.

KARANTA: An kama 'Ahmed Musa' na bogi da laifin damfarar N700,000 a Kano

"Ana gab da fara gabatar da wannan shiri nan da yan kwanaki wanda ciki za'a nuna shugaba Buhari ba shine ke jagorantar ƙasar nan ba."

Adeshina ya bayyana cewa ba komai ya janyo wannan abu ba face "yaƙi da cin hanci da rashawa da samar da tsaro tare da farfaɗo da tattalin arziki da yake ta yi, kuma wannan ba zai ɗauke hankalin wannan gwamnati daga abinda ta sa a gaba ba."

Legit.ng ta rawaito cewa, a jihar Kano, jam'iyya mai mulki APC da babbar jam'iyyar hamayya ta PDP sun fara cacar baki musayar yawu akan zaɓen gwamna mai zuwa na shekarar 2023.

Jam'iyyar PDP, a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ta ce ba za ta lamunci duk wani wargi a zaɓen gwamna mai zuwa da sunan 'Inconclusive', watau zaben da bai kammalu, ba.

Ita kuwa jam'iyya mai mulki, APC, a ƙarƙashin shugabancin Abdullahi Abbas, ta sha alwashin sake maimaita wani 'Inconclusive' din tare da tafka maguɗi a kakar zaɓen shekarar 2023 mai zuwa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel