IGP Adamu ya shigar da karar dan takarar shugaban kasa a kan wallafa rahoton karya a kansa

IGP Adamu ya shigar da karar dan takarar shugaban kasa a kan wallafa rahoton karya a kansa

- IGP Mohammed Adamu, babban sifeton rundunar 'yan sanda, ya shigar da karar mai gidan jaridar SaharaReporter, Omoyele Sowore

- Adamu ya garzaya kotu ne tare da neman Sowore, tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, ya bashi hakuri a kan kazafin da ya yi masa

- Kotu ta tsayar da ranar 26 ga watan Janairun sabuwar shekara domin fara sauraron karar da IGP Adamu ya shigar

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta amince da karɓar karar da shugaban hukumar yan sanda, IGP Mohammed Adamu, ya shigar gabanta akan ɗan gwagwarmayar nan kuma mai gidan jaridar yanar gizo Sahara Reporters, Omoyele Sowore.

Mai shari'a, Binta Mohammed, ce ta amince da sauraron ƙarar wacce lauyan mai kara, Alex Izinyon, ya shigar inda suke neman kotu da ta ci tarar Sowore Naira biliyan 10 bisa rahoton karya da suke zarginsa da bugawa a jaridarsa, kamar yadda Daily Nigerian.

Lauya Izinyon, ya buƙaci kotu da ta "lamincewa mai ƙara, IGP Adamu, shigar da korafi kan wanda ake zargi, watau Sowore, wanda yake zaune a No. 1, Mosafejo Street, Kiribo, ƙaramar hukumar Ese-Odo, jihar Ondo."

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, ya rawaito inda IGP Adamu ya bayyana rahoton da shi Sowore ya buga a ranar 3 ga watan Agusta cewa yarfe ne da ƙage.

IGP Adamu ya shigar da dan takarar shugaban kasa a kan wallafa rahoton karya a kansa
IGP Adamu ya shigar da dan takarar shugaban kasa a kan wallafa rahoton karya a kansa
Source: UGC

Sowore dai ya buga labarin cewa, Shugaban yan sanda na ƙasa ya tattara wasu makudan kudade ta barauniyar hanya don gina wata makarantar horar da yan sanda a jihar Nasarawa.

IGP Adamu, ta bakin lauyansa, Izinyon, ya yi barazanar sai Sowore da kafar yaɗa labaransa sun ba shi biliyan goma bisa wannan maganar ko kuma su wallafa sakon neman afuwar sa a cikin kwana bakwai.

Mai shari'a Binta ta daga sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2021.

Legit.ng ta rawaito cewa a jihar Kano, jam'iyya mai mulki APC da babbar jam'iyyar hamayya ta PDP sun fara cacar baki musayar yawu akan zaɓen gwamna mai zuwa na shekarar 2023.

Jam'iyyar PDP, a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ta ce ba za ta lamunci duk wani wargi a zaɓen gwamna mai zuwa da sunan 'Inconclusive', watau zaben da bai kammalu, ba.

Ita kuwa jam'iyya mai mulki, APC, a ƙarƙashin shugabancin Abdullahi Abbas, ta sha alwashin sake maimaita wani 'Inconclusive' din tare da tafka maguɗi a kakar zaɓen shekarar 2023 mai zuwa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel