Labari mai dadi: ASUU ta bayyana ranar komawa bakin aiki

Labari mai dadi: ASUU ta bayyana ranar komawa bakin aiki

- Kungiyar malamai masu koyarwa ta jami'o'i, ta bayyana labarin komawarta a watan Janairu

- A wata wallafa da kungiyar ASUU ta yi a Twitter, ta ce za ta koma aiki idan FG ta cika bukatunta

- Kungiyar ta ce za ta janye yajin aikinta ne bayan FG ta biya dukkan albashin da malamai suke bin ta

Kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i (ASUU) a ranar Talata, 22 ga watan Disamban 2020, ta bada satar amsa a kan lokacin da za ta kawo karshen yajin aikinta na watanni 9.

Kungiyar ta sanar da hakan a wata wallafa da tayi a shafinta na Twitter.

Kamar yadda wallafa ta ce: "Labari mai dadi. Za a janye yajin aiki idan har gwamnatin tarayya ta biya dukkan albashin da malamai ke bin ta."

Idan za a tuna, a ranar Litinin, 21 ga watan Disamban 2020, gwamnatin tarayya ta ce dalibai za su koma azuzuwa a watan Janairun 2021.

KU KARANTA: Ku mayar da kudin da kuka karba na gangamin #BringBackOurBoys#, Garba Shehu

Labari mai dadi: ASUU ta bayyana ranar komawa bakin aiki
Labari mai dadi: ASUU ta bayyana ranar komawa bakin aiki. Hoto daga @ASUUNGR
Asali: Twitter

A yayin magana a kan komawa makaranta, ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da ASUU sun kai kashi 98 na fahimtar juna.

KU KARANTA: Neymar: Duba gidansa mai darajar N3.3bn da ke Paris tare da Ferrari din sa me darajar N130m

A wani labari na daban, bayan kwashe kusan shekara daya da kungiyar malamai masu koyarwa na jam'i'o'i suka yi a gida suna yajin aiki tare da hadin kan cutar korona, gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran malaman za su koma aji a watan Janairun 2021.

Ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba. Ya tabbatar da cewa sun kai wani mizanin daidaitawa da kungiyar malaman jami'o'in da ya kai kashi 98.

Ministan ya tabbatar da cewa ragowar kashi biyun ba wani abun dubawa ne, lamurra ne da za a iya hakuri da su. A kalamansa: "Mun cika burikan ASUU kusan kashi 98. Dan ragowar abubuwan da ba a rasa bane."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng