FEC: Gwamnatin Tarayya za ta kashe N8bn a gyaran titunan da su ka lalace

FEC: Gwamnatin Tarayya za ta kashe N8bn a gyaran titunan da su ka lalace

-An yi zaman mako-mako na Ministocin Tarayya jiya a Garin Abuja

-Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci wannan zaman

-FEC ta amincewa FERMA ta yi gyaran wasu titunan da su ka lalace

Majalisar FEC ta zauna a ranar Laraba, 23 ga watan Disamba, 2020, inda ta zartar da wasu matakai a fadar shugaban kasa na Aso Villa da ke birnin tarayya.

Jaridar The Eagle ta fitar da rahoto cewa majalisar ta amince cewa a batarda Naira biliyan 8.1 wajen gyaran wasu hanyoyi da su ka lalace cikin Najeriya.

Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Raji Babatunde Fashola ya bada wannan sanarwa a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa bayan taron.

Raji Babatunde Fashola SAN ya bayyana cewa jihohin da za su amfana da wannan aiki su ne: Akwa Ibom, Anambra, Kuros Riba, Nasarawa, sai kuma Legas.

KU KARANTA: FEC ta shigar da ayyukan tituna da jirgin saman Maiduguri

Haka zalika za a gyara wasu tituna da ke cikin Ogun, Kogi, Edo, Yobe, Delta, da birnin tarayya.

Ministan ya shaidawa manema labarai cewa a zaman FEC din, ma’aikatarsa ta gabatar da takarda a madadin hukumar FERMA mai alhakin gyaran hanyoyi.

Daga cikin titunan da za a gyara akwai na Ikot Ekpene-Itu da ke jihar Kuros Riba, sai kuma aikin hanyar Onitsha-Aguleri-Adani a jihar Anambra, inji Fashola.

Za a yi gyaran hanyar Nasarawa-Toto-Abaji, sannan za ayi aiki a hanyar Zuba-Abaji a garin Abuja.

KU KARANTA: Sabon rikici ya na jiran Gwamnati a kan biyan alawus din Jami'o'i

FEC: Gwamnatin Tarayya za ta kashe N8bn a gyaran titunan da su ka lalace
Minista Babatunde Fashola Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

Har ila yau Ministan ya ce akwai facin da za ayi a titin Atan-Agbara da ke tsakanin Legas da Ogun, da kuma titin Okene-Adogo-Ajaokuta-Itobe da ke jihar Kogi.

Sannan Ministan yace FERMA za ta taba hanyoyin Potiskum-Fika-Ngalda-Gombe, da na Ogbogui-Abangbe, da Benin-Asaba-Onitsha, da kuma titin Warri-Benin.

Jiya kun ji Gwamnatin Tarayya ta na la’akari da makwabtanta kafin ta haramta jiragen saman Ingila sauka ko tashi a Najeriya saboda sake barkewar COVID-19.

Gwamnatin Najeriya tace ba ta so ta yi garajen rufe iyakokinta saboda annobar cutar Coronavirus.

Lai Mohammed ya ce abin da zai faru idan shugaban kasa ya hana jiragen Ingila tashi ko sauka, shi ne za a koma kewaye Najeriya, ana zuwa Landan ta makwabta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel