Najeriya na sauraron Togo, Ghana da Benin kafin ta dauki mataki a kan Ingila

Najeriya na sauraron Togo, Ghana da Benin kafin ta dauki mataki a kan Ingila

- Gwamnatin Tarayya tace ba za tayi saurin hana jiragen Ingila sauka ko tashi ba

- Gwamnati ta ce yin hakan zai sa wasu su koma bin jiragen Benin, Togo ko Ghana

- Lai Mohammed ya na ganin wannan mataki zai iya taba tattalin arzikin Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce ta zurawa makwabtanta idanu ne kafin ta dauki mataki game da hana jirgi tashi daga ko sauka a kasar Ingila.

Jaridar Vanguard ta rahoto Ministan yada labarai da al’adu na kasa ya na wannan bayani a jiya.

A cewar gwamnatin tarayyar, akwai bukatar samun hadin-kai tsakanin Najeriya da kuma kasashen da ta ke makwabtaka da ita a kan lamarin.

Da aka yi hira da Lai Mohammed, a shirin siyasar kasa gidan rediyon tarayya a Abuja, ya bayyana cewa ba su so su yi gaggawar daukar wani mataki.

KU KARANTA: Musulmai su fara tanadin kudin hajji - Gwamnan Legas

Najeriya na sauraron Togo, Ghana da Benin kafin ta dauki mataki a kan Ingila
Ministan yada labarai da al’adu Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

Alhaji Lai Mohammed ya ce: “Ko da yake gwamnati ta damu da shigo da sabon nau’in COVID-19 cikin Najeriya, ba ta son yin aikin garaje.”

Lai Mohammed ya bayyana cewa kwamitin PTF ya yanke hukuncin cewa za ta sa ido, ta ga abin da ke faruwa, kafin a kai ga daukar wani mataki.

“Ba mu so mu yi saurin daukar matakin hana jirgin Ingila tashi ko sauka a Najeriya, sai kuma mu ga ana shigo mana ta Cotonou, Lome ko Accra."

“Hakan zai kawowa ‘yan Najeriya wahala domin za ka kai dukiya zuwa wata kasa, ka yi asarar kudi.” Lai ya na tsoron fasinjojin su canza hanya.

KU KARANTA: Babu dokar kulle a Najeriya

Ministan ya ce jama’a za su iya yin dabara su shiga wadannan kasashe ta iyakokin kasa, sai su nemi jirgin sama daga can da zai shiga da su Ingila.

A yau kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara nazari a game da yiwuwar sake rufe iyakokin kasar bayan budewar da tayi a kwanan nan

Gwamnatin tarayyar ta ce za ta dauki matakin sake rufe iyakokin ne idan har matsalar rashin tsaro ya ci gaba da ta'azzara a fadin jihohin kasar.

Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ne ya bayyana hakan yayin da aka yi hira da shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel