Shugabanci ba wasa bane: Gwamna Badaru ya gargadi masu yi masa adawa, ya yi barazanar daukar mataki mai tsauri

Shugabanci ba wasa bane: Gwamna Badaru ya gargadi masu yi masa adawa, ya yi barazanar daukar mataki mai tsauri

- Mohammad Badaru Abubakar, gwamnan jihar Jigawa, ya gargadi masu yi masa adawa da sukar manufofin gwamnatinsa

- Gwamna Badaru ya ce shiru-shiru ba tsoro bane ko rashin wayo, a saboda haka ba zai cigaba da jurar zaginsa ba

- Badaru na shan suka a cikin jam'iyyarsa ta APC da wasu jam'iyyun da suka goyi bayan gwamnan don samun nasararsa a zaben 2019

Gwamna Mohammad Badaru Abubukar na jihar Jigawa, ya nuna matuƙar damuwarsa bisa yawan sukar da ya ke sha daga yan hamayya da ma wasu 'yan jam'iyyarsa ta APC kan manufofin gwamnatinsa.

Da yake martani jim kaɗan bayan rantsar da shugabannin riƙo na jam'iyyar APC, gwamna Badaru ya ce, shuru-shuru a shugabanci fa ba tsoro ko rashin wayo ba ne, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Ya bayyana cewa yan siyasa a jihar Jigawa na amfani da saukin kansa suna zaginsa da sukar duk wata manufa mai kyau a jihar.

KARANTA: Kage da kazafi: IGP Adamu ya shigar da karar dan takarar shugaban kasa a 2019

A kalaman nasa ya ce, "Wasu 'yan siyasar sun raina ni har suke samun damar zagina, suna kushe duk wani shiri da manufa, wanda ba wani shugaba da zai juri wannan shirmen.

"Daga yanzu, ba zan kara jure irin wannan zagi da wani ko wasu su cigaba da cin mutuncina da ta gwamnatin mu ba. Zan yi maganin kowaye, shugabanci ba abin wasa ba ne".

Shugabanci ba wasa bane: Gwamna Badaru ya gargadi masu yi masa adawa, ya yi barazanar daukar mataki mai tsauri
Shugabanci ba wasa bane: Gwamna Badaru ya gargadi masu yi masa adawa, ya yi barazanar daukar mataki mai tsauri @JGstategov
Asali: Twitter

KARANTA: Zulum ya rantsar da Farfesoshi biyu, masu PhD 2 a cikin shugabannin LGAs na Borno

Gwamna Badaru na shan suka a cikin jam'iyyarsa ta APC da wasu jam'iyyun da suka goyi bayan gwamnan don samun nasararsa a zaben gwamna kuma suke ganin yanzu gwamnan na yin gwamnati ba da su ba.

Gwamnan ya fitar da gargadin cewa, "Rashin kiyaye wannan shawara, to kuwa mutum zai yi mummunar nadama, kamar yadda na gaya muku zan bar ofishina na koma harkar kasuwancina, idan jam'iyya ta fadi ku zargi kanku ni bani da asara."

A jihar Kano, Legit.ng ta rawaito cewa jam'iyya mai mulki APC da babbar jam'iyyar hamayya ta PDP sun fara cacar baki musayar yawu akan zaɓen gwamna mai zuwa na shekarar 2023.

Jam'iyyar PDP, a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ta ce ba za ta lamunci duk wani wargi a zaɓen gwamna mai zuwa da sunan 'Inconclusive', watau zaben da bai kammalu, ba.

Ita kuwa jam'iyya mai mulki, APC, a ƙarƙashin shugabancin Abdullahi Abbas, ta sha alwashin sake maimaita wani 'Inconclusive' din tare da tafka maguɗi a kakar zaɓen shekarar 2023 mai zuwa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel