Kano: APC da PDP sun fara musayar yawu a kan zaben kujerar gwmna a 2023

Kano: APC da PDP sun fara musayar yawu a kan zaben kujerar gwmna a 2023

- Har yanzu da sauran shekaru biyu masu kwari kafin gudanar da zabukan shekarar 2023

- Amma duk da hakan sai ga shi cacar baki da musyar yawu mai zafi ta barke a kan zaben kujearar gwamna a jihar Kano

- A yayin da PDP ta bayyana cewa ba za ta sake yarda da salon zaben 'Inconclusive' ba, APC ta ce za ta murde zaben baki daya

A jihar Kano, jam'iyya mai mulki APC da babbar jam'iyyar hamayya ta PDP sun fara cacar baki musayar yawu akan zaɓen gwamna mai zuwa na shekarar 2023,kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Jam'iyyar PDP, a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ta ce ba za ta lamunci duk wani wargi a zaɓen gwamna mai zuwa da sunan 'Inconclusive', watau zaben da bai kammalu, ba.

Ita kuwa jam'iyya mai mulki, APC, a ƙarƙashin shugabancin Abdullahi Abbas, ta sha alwashin sake maimaita wani 'Inconclusive' din tare da tafka maguɗi a kakar zaɓen shekarar 2023 mai zuwa.

KARANTA: Facebook: Ango ya dakatar da daurin aure bayan amarya ta yi katobarar cewa za ta iya cin amanar aure akan N1m

Abbas, ya yi wannan furucin ne, a matsayin mayar da martani ga kalaman tsohon gwamna Kwankwaso, lokacin rantsar da sabbin shugabannin jam'iyyar APC a gidan gwamnatin Kano a yammacin ranar Talatar.

Kano: APC da PDP sun fara musayar yawu a kan zaben kujerar gwmna a 2023
Kano: APC da PDP sun fara musayar yawu a kan zaben kujerar gwmna a 2023 @Dawisu
Source: Twitter

Abdullahi Abbas ya ce, "Kwankwaso ya sha alwashin zaɓe mai zuwa sai dai a mutu ko a yi rai, to ba damuwa, muna shirye da hakan mu ma. Ai mu ba matsorata ba ne. Mun shiryawa yaƙin. Ba ma tsoron a mutu.

KARANTA: Harin Jakana ya fusata Zulum, ya yi wa rundunar soji wata tambaya mai muhimmanci

"Magoya bayan jam'iyyarmu, kar ku ragawa Kwankwaso shi da magoya bayansa. Idan suka zage ku a radiyo ko a waje, kar ku raga musu.

"Kai bari na gaya muku gaskiya, sai ma mun murde zaben 2023 kuma babu abinda zai faru. Za mu nunka abinda mu ka yi a mazabar Gama babu abinda aka isa a yi. Wannan lokacinmu ne. Gwamnatinmu ce." In ji Abdullahi Abbas shugaban jam'iyyar APC.

Legit.ng ta rawaito cewa Nasir El-Rufa'i, gwamnan Kaduna, ya sauke sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar 23 a ranar Talata

Kazalika, gwamnan ya sauke shugaban hukumar CSDA tare da maye gurbinsa da Sauda Amina-Ayotebi

Gwamnan ya ce an yi sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati a jihar Kaduna.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel