Yau ake sa ran Shugabannin ASUU za su yi taro da wakilan Gwamnati a Abuja

Yau ake sa ran Shugabannin ASUU za su yi taro da wakilan Gwamnati a Abuja

- Shugabannin kungiyar ASUU za su zauna da wakilan Gwamnatin Tarayya

- Idan an yi dace za a shawo kan yajin-aikin da aka dade ana ta yi a Jami’o’i

- Wannan shi ne karo na biyu da bangarorin da za su zauna a cikin kwana 5

A ranar Talata, 22 ga watan Disamba, 2020, gwamnatin tarayya za ta koma tattaunawa da kungiyar ASUU da ke faman yajin-aiki a Najeriya.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto dazu nan cewa an koma dakin taro na sulhu da shugabannin kungiyar malaman jami’ar ne a yau ranar Talata.

The PUNCH ta ce wakilan ASUU da bangaren gwamnatin tarayya sun hadu a birnin tarayya Abuja ne domin su tattauna kamar yadda su ka saba.

Ministan kwadago da samar da aikin yi na kasa, Chris Ngige shi ne wanda ya ke jagorantar wakilan da su ka fito daga bangaren gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Kungiyar ASUU za ta gana da Gwamnati

A gefe guda kuma Farfesa Biodun Ogunyemi shi ne wanda ya ke jagorantar bangaren kungiyar ASUU.

Da aka yi magana da Biodun Ogunyemi a jiya, ya yi watsi da duk abin da Ministan kwadago ya fada, ya ce ba zai yi magana ba sai gobe (Laraba).

Ya ce: “Game da abin da shi (Chris Ngige) ya ke fada, ba zan ce komai ba. Mu na duba lamarin.”

Sanata Chris Ngige a madadin gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa za su biya malaman jami’an da ke yajin-aiki, albashin da su ke bi bashi.

KU KARANTA: ASUU za ta janye yajin-aiki

Yau ake sa ran Shugabannin ASUU za su yi taro da wakilan Gwamnati a Abuja
Shugaban kasa da wakilan ASUU Hoto: www.tvcnews.tv
Asali: Twitter

Daga cikin alkawarin da aka yi wa ‘yan kungiyar ASUU, za a biya makudan kudin gyaran jami’o’i.

Kafin yanzu kun ji cewa malaman sun zauna da gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, inda aka shafe sa’a biyar amma ba tare da an samu matsaya ba.

Kawo yanzu babu wanda ya yi wa manema labarai bayanin sakamakon wancan taro da aka yi tsakanin shugabannin ASUU da gwamnatin kasar.

Tun a watan Maris aka rufe jami'o'in gwamnati, har yanzu an gaza shawo kan malaman makarantar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel