Da duminsa: An shiga ganawa tsakanin ASUU da Gwamnatin, da yiwuwan a janye yajin aiki yau

Da duminsa: An shiga ganawa tsakanin ASUU da Gwamnatin, da yiwuwan a janye yajin aiki yau

- Da yiwuwan a cimma matsaya a zaman da gwamnati ke yi da ASUU yau Juma'a

- A makon da ya gabata, gwamnati ta hakura da wasu abubuwa kuma ta kara kudi

- ASUU ta bukaci a bata mako daya domin tattaunawa da mambobinta

Gwamnatin tarayya a ranar Juma'a ta cigaba da tattaunawa da kungiyar malaman jami'o'inNajeriya ASUU domin kawo karshen yajin aiki wata takwas dake gudana.

Ganawar ranar Juma'a, da aka shirya farawa karfe 11 na safe bai yiwu ba sai misalin karfe 2:25 ba sallar Juma'a kuma Ministan Kwadago, Chris Ngige, ke jagorantan zaman.

Ya ce gwamnati ta yiwa kungiyar tayin wasu abubuwa makon da ya gabata kuma "sun yi alkawarin tattaunawa da mambobinsu kafin suk dawo mana da amsa."

KU KARANTA: PDP: Kotu ta dakatar da aikin shugabannin rikon kwarya a Jihar Ebonyi

Da duminsa: An shiga ganawa tsakanin ASUU da Gwamnatin, da yiwuwan a janye yajin aiki yau
Da duminsa: An shiga ganawa tsakanin ASUU da Gwamnatin, da yiwuwan a janye yajin aiki yau
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matawalle ya jinjina yiwuwar barin PDP, ya ce 'Ina fuskantar matsaloli; na yi wa Umahi murna'

Mun kawo muku cewa bayan watanni 8 ana muhawara, gwamnatin tarayya ta amince da bukatun kungiyar malaman jami'a ASUU cewa a togaciye mambobinta daga manhajar biyan albashi ta IPPIS.

A zaman da gwamnatin tayi da shugabannin ASUU ranar Juma'a, ta hakura kan wasu lamura wanda ya hada da wajabta biyan malaman ta IPPIS da kuma kar musu kudin alawus da kudin gyaran jami'o'i.

Yayin karanto abubuwan da suka tattauna bayan sa'o'i bakwai ana tattaunawa a dakin taron ma'aikatar kwadago, Ministan, Chris Ngige, ya ce gwamnati ta amince a biya mambobin ASUU albashinsu tun daga watan Febrairu zuwa Yuni da tsohon manhajar GIFMIS.

Hakazalika gwamnatin ta amince da kara kudin alawus na malaman daga N30bn zuwa N35bn, sannan kudin gyaran jami'o'i daga N20bn zuwa N25bn.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel