Yajin aiki: FG ta bayyana lokacin da jami'o'i za su koma

Yajin aiki: FG ta bayyana lokacin da jami'o'i za su koma

- Yajin aikin kungiyar malaman jami'o'i yana dab da cikewa shekara daya cif amma ya zo karshe

- Wannan tabbacin ya zo ne bayan gwamnatin tarayya ta bada sanarwa mai muhimmaci a ranar Litinin

- Gwamnatin tarayyar ta ce ta kai wata gaba da hankalinta ya kwanta cewa kungiyar ASUU ta kusa janyewa

Bayan kwashe kusan shekara daya da kungiyar malamai masu koyarwa na jam'i'o'i suka yi a gida suna yajin aiki tare da hadin kan cutar korona, gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran malaman za su koma aji a watan Janairun 2021.

Ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba.

Ya tabbatar da cewa sun kai wani mizanin daidaitawa da kungiyar malaman jami'o'in da ya kai kashi 98.

Yajin aiki: FG ta bayyana lokacin da jami'o'i za su koma
Yajin aiki: FG ta bayyana lokacin da jami'o'i za su koma. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

KU KARANTA: Ceton yaran Kankara: Wasu mutane suna cike da bakin ciki, Hadimin Buhari

Ministan ya tabbatar da cewa ragowar kashi biyun ba wani abun dubawa ne, lamurra ne da za a iya hakuri da su.

A kalamansa: "Mun cika burikan ASUU kusan kashi 98. Dan ragowar abubuwan da ba a rasa bane.

"A don haka nake fatan cikin daren yau mu kammala sauran ayyukan da ya dace mu yi. Su ma suna da wasu kananun ayyukan da ya dace su yi da jama'arsu.

"A ranar Talata muke sa rana za mu hadu da rana sannan mu sake tattaunawa. Akwai yuwuwar mu kawo karshen yajin aiki idan muka hadu gobe."

KU KARANTA: Muna da tabbacin Buhari zai kawo karshen rashin tsaro, Gwamnonin APC

A wani labari na daban, taron da FG da ASUU suka yi a ranar Alhamis wanda kowa yayi fatan za a cimma gaci ya kare ba tare da wata nasara ba.

Ya kamata a fara taron sirrin da misalin 4pm a dakin taron ma'aikatar kwadago da ayyuka, amma sai 5:20pm aka fara, sannan aka gama 8:18pm, sannan wadanda suka halarci taron sun ki sanar da manema labarai abinda suka tattauna.

Kafin a fara taron, ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, ya ce rashin halartar taron da wuri yana da nasaba da rashin karasa tuntubar ma'aikatar kudi sai safiyar Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel