Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo daga Umrah

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya dawo daga Umrah

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari tare da iyalinsa, Hajiya Aisha Buhari, sun dira babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja.

Hadimin shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan da yammacin nan inda yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari da uwargidarsa, Aisha Buhari sun dawo Abuja da yamman nan babyan gabatar da ibadar Umrah a Makkah, kasar Saudi Arabiyya."

Source: Legit.ng

Online view pixel