Uwargidar Buhari ta nemi Shugabanni su rika ɗaukar shawarar jama'a

Uwargidar Buhari ta nemi Shugabanni su rika ɗaukar shawarar jama'a

Hajiya Aisha Buhari ta ɗaura wani bidiyo a shafin ta na Tuwita wanda ya ke ta faman jawo magana a halin yanzu. A Ranar Juma’a 24 ga Watan Mayun 2019 ne Matar shugaban kasar tayi wannan aiki.

Aisha Buhari ta saka wani bidiyo ne na babban ‘dan siyasar nan na Kasar Afrika ta Kudu mai suna Julius Malema, inda yake ba sabon shugaban kasar watau Cyril Ramaphosa wasu muhimman shawarari.

Julius Malema ya ja-kunen shugaba Cyril Ramaphosa ne a lokacin da aka rantsar da shi a kan mulki kwanaki, da ya bi a hankali da wasu manyan na-kusa da shi da ka iya kai sa su kuma baro sa.

Malema ya fadawa shugaban kasar Afrikan ta Kudu cewa ka da ya biyewa ‘yan kanzagin da za su rika fada masa abin da ba gaskiya ba. Malema yace shugaban yana bukatar masu fada masa gaskiya a gefensa.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta caccaki wata Hadimar Shugaban kasa

Uwargidar Buhari ta nemi Shugabanni su rika ɗaukar shawarar jama'a
Aisha Buhari ta saba kokawa a kan wasu da su ka zagaye shugaban kasa
Source: Depositphotos

‘Dan siyasar ya kara da cewa akwai masu hurewa shugabanni kunne su rika fada masu sun yi daidai ko da kuwa sun yi abin da ya sabawa dokar kasa ko kuma hukuncin kotu, yace ya guji wannan mutane.

Hajiya Aisha Buhari tayi na’am da wannan jawabi na Julius Malema inda ta sake saka bidiyon a shafin ta tana mai karin bayani da nuni da cewa ya kamata shugabanni su ka rika daukar shawarar al’umma.

Matar shugaban kasar ta kuma nemi shugabanni su rika yin aiki tare. Hakan na zuwa ne mako guda bayan shugaba Buhari ya dawo daga Umrah tare da Iyalin na sa da kuma wasu na-hannun damansa.

Jama’a su na ta faman magana a kan wannan lamari a yanzu haka ganin cewa shugaban kasar yana tare da Maman Daura da Isa Funtua har a kasar Saudi a makon jiya, wanda ake tunani su su ka zagaye sa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel