Yajin aiki: Abinda aka tattauna tsakanin ASUU da FG a dogon zamansu
- Alamu sun nuna cewa taron sirri da gwamnatin tarayya da ASUU suka shiga a ranar Alhamis bai haifar da da mai ido ba
- Taron da suka yi a dakin taron ma'aikatar kwadago da ayyuka, wanda kafin su fara taron duk sun sakankance a kan za su daidaita
- Sai dai bayan fitowarsu daga taron, da misalin 8:18pm, sun ki sanar da manema labarai gaskiyar yadda ta kaya tsakaninsu
Taron da FG da ASUU suka yi a ranar Alhamis wanda kowa yayi fatan za a cimma gaci ya kare ba tare da wata nasara ba.
Ya kamata a fara taron sirrin da misalin 4pm a dakin taron ma'aikatar kwadago da ayyuka, amma sai 5:20pm aka fara, sannan aka gama 8:18pm, sannan wadanda suka halarci taron sun ki sanar da manema labarai abinda suka tattauna.
Kafin a fara taron, ministan kwadago da ayyuka, Chris Ngige, ya ce rashin halartar taron da wuri yana da nasaba da rashin karasa tuntubar ma'aikatar kudi sai safiyar Alhamis.
KU KARANTA: BringBackOurBoys: CNG ta isa Katsina, za ta fara zanga-zangar sai 'baba ta gani'
Kamar yadda yace: "Ya kamata mu da muke bangaren gwamnati mu tuntubi masu ruwa da tsaki, kuma har safiyar Alhamis ba mu gama hakan ba. Za mu fara taron a makare ne saboda har safiyar nan ba mu karasa tuntubar ma'aikatar kudi ba."
Ngige ya ce ya sakankance da taron. Sannan shugaban ASUU, Biodun Ogunyemi ya ce shima ya sakankance kamar yadda ministan ya sakankance.
"Da zarar mun kai matsaya, a shirye ma'aikatanmu suke da su koma wuraren ayyukansu," a cewarsa.
KU KARANTA: Kalamai masu ratsa zuciya da Zahra Buhari tayi ga mijinta a cikarsu shekaru 4 da aure
Ya ce yana fatan gwamnati za ta zo da al'amarin da zai janyo daidaitawa tsakaninta da kungiyar, don su koma bakin aikinsu.
A wani labari na daban, wani dan majalisar wakilai, Sam Onuigbo ya bar jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC, Premium Times ta wallafa.
Dan majalisar, mai wakiltar mazabar Ikwuano/Umuahia da ke jihar Abia, ya bayyana canja shekarsa ta wata wasika wacce kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya karanta a ranar Alhamis.
Kamar yadda aka saba, shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu ya bayyana rashin amincewarsa dangane da canja shekar Onuigbo, inda ya bukaci kakakin ya kwace kujerar, bukatar da bata samu karbuwa ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng