NCP ta kai Atiku Abubakar kotun Abuja a kan zargin bashin N500, 000, 000 a 2019

NCP ta kai Atiku Abubakar kotun Abuja a kan zargin bashin N500, 000, 000 a 2019

-Nigerian Continuity Progressive ta na ikirarin tana bin Atiku Abubakar bashi

-Kungiyar tace tayi wa ‘Dan takarar PDP aiki a zaben 2019, amma bai biya ba

-Lauyoyi sun shigar da kara, suna neman a tatso musu kudinsu daga hannunsa

Wata kungiyar zamantakewa da siyasa, Nigerian Continuity Progressive (NCP) ta shigar da karar Atiku Abubakar a gaban babban kotun tarayya a Abuja.

Kungiyar NCP ta na ikirarin cewa ta na bin Alhaji Atiku Abubakar bashin kudi N500, 000, 000.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar 18 ga watan Disamba, 2020, NCP tace tana bin ‘dan siyasar bashi ne daga yakin neman zaben 2019.

Takardun sammacin da su ka fito daga Magatakardan kotun tarayyar, Danmusa Williams, sun tabbatar da cewa ana karar tsohon mataimakin shugaban kasar.

KU KARANTA: Atiku zai iya takara a 2023 - PDP

NCP a kara mai lamba ta CU/2065/200, ta na tuhumar Atiku Abubakar, da wani jagora wajen yakin neman zaben shugaban kasar da ya yi a 2019, Dr. Nat Yaduma.

Kungiyar ta ce Atiku Abubakar wanda ya rike tutar jam’iyyar PDP a zaben da ya wuce, da Nat Yaduma sun hana ta kudin aikin da ta yi masu na shekaru biyu.

Kotun da ke zama a Abuja ta zartar da cewa idan har Atiku da Yaduma ba su bayyana gabanta zuwa lokacin da aka ce ba, za a ba kungiyar kudin da ta ke bi.

Bayan haka za a bukaci jirgin yakin Atiku su biya NCP kudi a dalilin ci mata zarafi da aka yi. Morris O. Osakwe shi ne wanda ya tsayawa kungiyar gaban kotu.

KU KARANTA: Garba Shehu: Buhari ya kashe badakalar 10% a kwangiloli bayan hawa mulki

NCP ta kai Atiku Abubakar kotun Abuja a kan zargin bashin N500, 000, 000 a 2019
Atiku Abubakar Hoto: www.instagram.com/atikulated
Source: Instagram

Lauyoyin bangaren Atiku Abubakar sun ki amsa tuhumar da ake yi masu. Da aka tuntubi Hadimin ‘dan siyasar da jam’iyyar PDP, sun ki su ce wani abu.

A baya kun ji cewa game da rikicin PDP, uwar Jam’iyya ta raba gardamar da ke tsakanin bangaren Amb. Aminu Wali da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Majalisar NWC ta PDP ta sallamawa ‘Yan Kwankwasiyya, yayin da ‘Yan taware suka fito suka ce sun kori tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso daga jam'iyya.

A wani jawabi, shugabannin PDP sun ba sashen Rabiu Kwankwaso gaskiya a rikicin cikin-gidan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel