COVID 19: Ku haramta jiragen Birtaniya zuwa Nigeria, Atiku ya shawarci Buhari

COVID 19: Ku haramta jiragen Birtaniya zuwa Nigeria, Atiku ya shawarci Buhari

- Atiku Abubakar ya gargadi gwamnatin Najeriya ta hana zirga zirgan jiragen sama tsakanin Najeriya da Birtaniya

- Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce hakan ya zama dole ne domin dakile yaduwar sabon nau'in annobar korona ta da bulla a Landan

- Tuni dai, an fara samun hauhawar alkallumar masu kamuwa da cutar ta korona a jihohin Najeriya

Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ya dora laifin samun hauhawar annobar COVID 19 a baya bayan nan kan gwamnatin tarayya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya shawarci gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa don kare rayukan 'yan Najeriya daga annobar COVID 19.

Ya shawarci gwamnatin tarayya ta yi koyi da wasu kasashen Turai da suka hana jirage daga Birtaniya zuwa kasashensu.

COVID 19: Ku haramta jiragen Birtaniya zuwa Nigeria, Atiku ya shawarci Buhari
COVID 19: Ku haramta jiragen Birtaniya zuwa Nigeria, Atiku ya shawarci Buhari. Hoto: @atiku
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Sai dai 'a mutu ko a yi rai' a Kano, ba zamu yarda da 'inconclusive' ba, Kwankwaso

Jigon na jam'iyyar PDP ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai taken: 'Rigakafi ya fi magani' wacce ya fitar ranar Lahadi a Abuja dauke da sa hannunsa.

Atiku ya ce, 'Dole mu fada wa kanmu gaskiya domin bangaren kiwon lafiyanmu bata shirya wa irin wannan anobar ba. Mun riga mun rasa rayyuka a baya. Babu bukatar hakan ya sake faruwa.

"Tuni, wasu kasashen suka dauki mataken gaggawa kuma ya zama dole Najeriya ta dauki mataken kare kanta duba da irin zirga zirgan jiragen tsakanin Najeriya da Landan inda sabon na'iun cutar korona mai hadari ya bulla.

"Abinda yasa cutar ta yi wa Najeriya illa sosai a karon farko shine gwamnatin tarayya ta ki daukan mataki duk da gargadin da 'yan Najeriya da dama suka yi ciki har da na cewa ta rufe iyakokinta kafin cutar da zama annoba.

"Abinda ya faru a 2020 ya kamata ya zama darasi. Don haka, bai kamata mu sake maimaita abinda ya faru a baya ba.

KU KARANTA: Sule Lamiɗo: PDP ce kaɗai zata iya warware matsalolin Nigeria

"Sabon na'iun COVID da ya bulla a Birtaniya akasari Landan na iya durkake bangaren lafiyar Najeriya idan bamu dauki matakin kare kanmu cikin gaggawa ba ta hanyar hana jirage daga Birtaniya sauka a Najeriya har sai an shawo kan wannan sabon nau'in kwayar cutar. A kan wannan batun, rigakafi ya fi magani."

A baya, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 1 a kasafin 2021 don ginawa da gyara masallatan juma'a, makarantun islamiyya, makabartu, wuraren wa'azi da sauran harkokin addini.

Kwamishinan harkokin addinan jihar, Sheik Tukur-Jangebe ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Juma'a bayan gabatar da kasafin ma'aikatar na 2021 ga majalisar dokokin jihar Zamfara.

Jangebe ya shaida cewa gwamnatin Zamfara ta tsara ayyukan ci gaba a karkashin ma'aikatar addinin musulunci a 2021.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel