Rundunar soji ta bayyana dalilin Shekau na yin ikirarin cewa Boko Haram ce ta sace daliban Kankara
- Rundunar soji ta fito ta yi bayani dalla-dalla kuma daki-daki dangane da yadda ta kubutar da daliban sakandiren Kankara
- Bayan sace daliban a ranar 11 ga watan Disamba, kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin sace daliban
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana salon da ta bi na ceto yaran makarantar sakandire ta kimiyya dake ƙanƙara su 344 waɗanda yan ta'adda suka sace ranar 11 ga Disamba.
Kazalika, ta mayar da martanai ga ikirarin shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, akan cewa kungiyarsa ce keda alhakin sace daliban.
A cewar rundunar Sojin, ta yi amfani da salo wajen kubutar da yaran don tabbatar da cewa babu wani yaro da aka kashe ko ya ji rauni a hannun 'yan ta'addar, kamar yadda Punch ta rawaito.
Mai magana da yawun rundunar soji a kafafen yaɗa labarai, Manjo Janar John Enenche, tare da tsohon darekta a bangaren amfani da hikimomin yaƙi, Manjo Janar Ahmed Jibrin mai ritaya, sune su ka bayyana hakan.
KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su
Manyan sojojin sun fadi hakan ne yayin wani shiri na musamman na gidan talabijin din kasa (NTA) mai taken "Good Morning Nigeria".
Janar Jibrin ya ce, sakamakon sace ɗaliban, minista da manyan jami'an tsaron tare da mai bada shawara kan harkar tsaro sun dira a garin Ƙanƙara.
Ministan tsaro ya bayar da ka'idojin da za'a bi don tabbatar da kowanne yaro ya kubuta ba tare da cutarwa ba.
Da ya ke mayar da martani a kan ikirarin Abubakar Shekau, shugaban Boko Haram, a kan cewa kungiyarsa keda alhakin sace alhakin daliban, Jana Jibrin ya ce;
“Shekau ba shi da damar da zai iya wannan aikin sakamakon kokarin kawar da mayakansa da rundunar Soji ke yi a Arewa maso Gabas."
A cewar Manjo Jibrin, Shekau mutum ne mai ƙi-faɗi da ke son yin amfani da damar sace yaran don kawo hayaniya da rudani.
Kazalika, ya bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da iƙirarin Shekau akan batun garkuwa da daliban sakandiren Kankara.
Wasu 'yan Najeriya na ganin cewa zai yi matukar wahala ace ba'a rasa rayukan wasu daliban ba da kungiyar Boko Haram ce ta sacesu.
Sannan sun kara da cewa rundunar soji za ta fuskanci gagarumar turjiya wajen mayakan Boko Haram da ace sune suka sace daliban makarantar sakandiren kimiyya da ke Kankara.
Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa kotun ICC mai tuhumar manyan laifukan ta'adddanci a duniya ta zubar da dan takarar Nigeria, Jastis Ishaq Bello.
Kotun ta shawarci Jastis Bello, dan takarar Nigeria da Buhari ya zaba, bayan ya samu kuri'u a zagayen zabe na farko da kuma samun kuri'u a zagaye na biyu na zaben.
ICC za ta zabi sabbin alkalai 6 ne daga cikin jimillar alkalai 18 da kotun, wacce ke kasar Geneva Switherland, ya kamata ta mallaka.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng