Habu Galadima: Darekta Janar na NIPSS ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya

Habu Galadima: Darekta Janar na NIPSS ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya

- Allah ya yiwa Farfesa Habu Shuaibu Galadima, shugaban cibiyar NIPSS, rasuwa da safiyar ranar Lahadi

- Darekta a NIPSS, C. F. J Udaya, ne ya sanar da mutuwar Farfesa Galadima a cikin wani sako da ya wallafa da yammacin ranar Lahadi

- Ya ce marigayi Farfesa Galadima ya yi mutuwar fuj'an da safiyar ranar Lahadi bayan takaitacciyar rashin lafiya

Farfesa Habu Shuaibu Galadima, darekta janar a cibiyar horon manyan ma'aikata a kan sanin makamar aiki (NIPSS) da ke Kuru, Jihar Filato, ta rasu.

C. F. J Udaya, darektan gudanarwa da kula da a al'amuran ma'aikatan NIPSS, ne ya sanar da hakan a cikin wani sako da ya wallafa da yammacin ranar Lahadi, kamar yadda TheCable ta wallafa.

A cewar Udaya, Galadima ya rasu bayan takaitacciyar rashin lafiya kuma za'a binne shi bisa tsarin addinin Musulunci.

"Amadadin shugabanni da dukkan sauran ma'aikatan NIPSS, mu na masu bakin cikin sanar da mutuwar fuj'an da ta samu shugaba/CEO na NIPSS, Farfesa Habu Shuaibu Galadima da afiyar ranar Lahadi, 20 ga watan Disamba, sakamakon takaitacciyar rashin lafiya," a cewar Udaya.

KARANTA: Korona: El-Rufa'i ya dauki sabon mataki da ya shafi ma'aikata, Masallatai, da Cocinan Kaduna

Udaya kara da cewa; "za'a yi jana'izarsa bisa tsarin addinin Musulunci."

Habu Galadima: Manajan Darekta na NIPSS ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya
Habu Galadima: Manajan Darekta na NIPSS ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya
Source: UGC

Marigayi Galadima ya karbi kujerar shugabancin NIPSS a Watan Yulin shekarar 2019 bayan majalisar ta tabbatar da shi.

Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa kotun ICC mai tuhumar manyan laifukan ta'adddanci a duniya ta zubar da dan takarar Nigeria, Jastis Ishaq Bello.

Kotun ta shawarci Jastis Bello, dan takarar Nigeria da Buhari ya zaba, bayan ya samu kuri'u a zagayen zabe na farko da kuma samun kuri'u a zagaye na biyu na zaben.

ICC za ta zabi sabbin alkalai 6 ne daga cikin jimillar alkalai 18 da kotun, wacce ke kasar Geneva Switherland, ya kamata ta mallaka.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel