Bidiyon iyayen daliban Kankara suna jiran isowar 'ya'yansu
- Iyayen daliban makarantar Kankara ta gwamnati sun yi cincirindo suna jiran isar 'ya'yansu
- A jiya Alhamis ne aka ceto yaran da 'yan bindiga suka sace daga dakunan kwanansu a makaranta
- A safiyar Juma'a yaran suka isa gidan gwamnatin jihar Katsina inda suka gana da Masari da Buhari
Cike da farin ciki tare da mika godiya ga Ubangiji, iyayen daliban makarantar gwamnati ta Kankara da aka sace a ranar Juma'a sun taru a farfajiyar makarantar.
Hakan ta faru ne bayan da aka cteo daliban da 'yan bindiga suka sace a ranar Juma'a da ta gabata a garin Kankara.
Bayan samun ceto daliban, an garzaya da su gidan gwamnatin jihar Katsina da safiyar yau Juma'a.
Daga nan ne suka gana da gwamnan jihar Katsina, Bello Masari tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
KU KARANTA: Barkewar korona karo na 2: Sama da mutum 1,000 sun sake harbuwa
Kamar yadda bidiyon da jaridar The Cable ta wallafa ya nuna, iyayen daliban sun cika dankam a farfajiyar makarantar suna jiran isowar 'ya'yansu cike da farin ciki.
KU KARANTA: 2023: Sunayen shugabannin kamfen da Atiku ya kaddamar a jihohi 36
A wani labari na daban, daliban GSSS Kankara na jihar Katsina da 'yan bindiga suka sace sun iso gidan gwamnati. Jami'an tsaro ne suka yi musu iso har cikin gidan gwamnatin jihar Katsina.
A ranar Juma'a ne 'yan bindiga suka afka GSSS Kankara da ke jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da daruruwan dalibai makarantar, bayan isar Shugaba Muhammadu Buhari Daura, garinsa na haihuwa da sa'o'i kadan.
dan ba a manta ba, gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ya ce harin ya ritsa da dalibai 333 da ke makarantar, Thisday ta wallafa.
A wata takarda da fadar shugaban kasa ta saki, ta ce an gano inda daliban suke, kuma suna cikin koshin lafiya. Kamar yadda takardar tazo, ana cigaba da tattaunawa da wadanda suka saci yaran.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng