Rashin tsaro: Sarkin Anka ya bukaci FG ta lamunce wa jama'a su dinga yawo da makamai
- Sarkin Anka, Attahiru Muhammad Ahmad Anka, ya bayyana alhininsa a kan rashin tsaron kasar nan
- Basaraken ya ce har shugabannin gargajiya basu tsira ba daga matsalar rashin tsaron Najeriya
- Sarkin ya ce idan ba a yi komai ba a kai, mutane za su fara rike makamai don kare kansu da kansu
Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad Anka, yace gara gwamnatin tarayya ta baiwa kowa damar daukar makamai don kare kansa akan matsalar rashin tsaron dake addabar Najeriya.
Shugaban gargajiyan ya bayyana hakan a wata takardar wacce ya bayyana alhininsa akan harin da aka kaiwa sarkin Kaura Namoda.
Sarkin wanda ya bayyana damuwarsa akan hare-haren da ake kai wa shugabannin gargajiya, inda yace har yanzu ba ayi wani abu ba don dakatar da hare-haren.
KU KARANTA: APC: Za mu tabbatar da cewa abinda ya faru a Kankara bai sake faruwa
Sarkin yace sun gaji da hakurin da ake bayar wa idan an kai wa sarakuna hari, idan ba ayi wani abu ba, yakamata mutane su fara daukar makamai don kare kawunansu.
A wani labari na daban, gagagrumar gobara ta tashi a kwalejin ilimi na jihar Zamfara da ke garin Maru inda ta lamushe dakunan kwanan dalibai mata da ke makarantar, jaridar The Punch ta wallafa.
KU KARANTA: 'Yan sanda sun hargitsa 'yan bindiga, sun ceto dalibai 84 da shanu 12 a Katsina
Dr. Abdullahi Haruna, daya daga cikin manyan shugabannin makarantar ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya hakan a garin Gusau a ranar Asabar.
Ya ce muguwar gobarar ta tashi ne a ranar Alhamis yayin da daya daga cikin daliban ke girki da risho dauke da kalanzir.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng