Da duminsa: Gobara ta lamushe dakunan kwanan dalibai a kwalejin ilimi ta Zamfara

Da duminsa: Gobara ta lamushe dakunan kwanan dalibai a kwalejin ilimi ta Zamfara

- Mummunan gobara ta tashi a rukunin dakuna kwanan dalibai mata da ke kwalejin ilimi na Zamfara

- Hakan ya faru ne sakamakon girki da risho dauke da kalanzir da daya daga cikin daliban take yi

- Kayayyakin miliyoyin naira sun salwanta amma ba a rasa rai ba kuma babu wanda ya samu rauni

Gagagrumar gobara ta tashi a kwalejin ilimi na jihar Zamfara da ke garin Maru inda ta lamushe dakunan kwanan dalibai mata da ke makarantar, jaridar The Punch ta wallafa.

Dr. Abdullahi Haruna, daya daga cikin manyan shugabannin makarantar ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya hakan a garin Gusau a ranar Asabar.

Ya ce muguwar gobarar ta tashi ne a ranar Alhamis yayin da daya daga cikin daliban ke girki da risho dauke da kalanzir.

KU KARANTA: Yaran Kankara: Shehu Sani ya bai wa FG shawara a kan yadda za ta bai wa makarantu kariya

Da duminsa: Gobara ta lamushe dakunan kwanan dalibai a kwalejin ilimi ta Zamfara
Da duminsa: Gobara ta lamushe dakunan kwanan dalibai a kwalejin ilimi ta Zamfara. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

Ya ce rukunin dakunan baccin daliban mata ya kunshi dakuna 20 kuma dukkansu sun kurmushe kurmus.

"Kayayyakin dalibai da suka hada da suturu, takardunsu, kayan gado da sauran kayan amfani na miliyoyin naira sun kone.

"Muna gode wa Allah babu wanda ya rasa rayuwarsa kuma babu wanda ya samu rauni. Hukumar makarantar ta samar da kayayyakin rage radadi ga daliban," ya bayyana.

Ya yi kira ga daliban da su kwantara da hankulansu sanna su kalla lamarain a matsayin kaddara daga allah.

ya roki gwamnatoci a kowanne mataki da su duba tare da tallafawa daliban da lamarain ya risata da su.

Ya kara da karyata jama'a da ke yadawa cewa miyagun 'yan bindiga ne suka bankawa dakunan kwanan daliban wuta, inda ya kwatanta hakan da labaran kanzon kurege wanda aka shirya domin batar da jama'a.

KU KARANTA: Matashiya mai kunar bakin wake ta tada bam, ta kashe mutum 3 a Borno

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane 6, da wata mata tare da wasu yara 6 a wani hari na mayar da martani a karamar hukumar Kauru, bayan harin Zangon Kataf da aka kai ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba, daren Alhamis, 'yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Zangon Kataf dake jihar Kaduna, inda suka kashe mutane 7.

A wata takarda da kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan, ya ce gwamnatin tace a karkashin taimakon rundunar Operation Safe Heaven da 'yan sanda, sun tabbatar wa da gwamnatin jihar Kaduna cewa rikicin ya faru ne tsakanin makiyayan Kauru da karamar hukumar Lere.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel