'Yan sanda sun hargitsa 'yan bindiga, sun ceto dalibai 84 da shanu 12 a Katsina
- 'Yan bindiga sun sake kai wa 'yan makaranta hari a karamar hukumar Dandume ta Katsina
- Sun kwashe daliban Islamiya yayin da suke dawowa daga Maulidi a garin Mahutan Dandume
- Tuni dai rundunar 'yan sandan jihar ta ceto daliban 84, wasu mutum 4 da shanu a dajin Danbaure
Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kwashe dalibai daga makarantar islamiya a garin Mahuta da ke karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina.
Kamar yadda jaridar Katsina Post ta wallafa, an kwashe daliban ne bayan sun kammala maulidi a Unguwar Al-Kasim da ke wani kauye a kusa da su.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace shugaban ma'aikata, sun halaka direbansa a Edo
Rundunar 'yan sandan jihar Kstina ta ceto dalibai 84 wadanda 'yan bindigan suka sace a garin Mahuta da ke karamar hukumar Dandume, Channels Tv ta wallafa.
Wannan ya biyo bayan kiran gaggawa da suka samu a ranar Asabar daga DPO na Dandume wanda ya sanar da cewa daliban Islamiyyar Hizburrahim guda 84 suna hannun 'yan bindiga.
A takardar da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya fitar a ranar lahadi, ya ce 'yan sandan sun ceto daliban,, wasu mutane hudu da kuma shanu 12 daga hannun 'yan bindigan da suka nufi dajin Danbaure da niyyar barin garin da su.
KU KARANTA: Hotuna: Cike da farin ciki, iyaye sun hadu da 'ya'yansu da aka sace a Kankara
A wani labari na daban, tsohon sanatan nan, Sanata Shehu Sani, ya bai wa jami'an tsaro hanyoyin kulawa da makarantu a arewacin Najeriya, Channels Tv ta wallafa.
Ya bayar da shawarwarin ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Asabar, bayan sace daruruwan daliban GSSS Kankara a jihar Katsina.
Sanata Shehu Sani, wanda ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya, yayi kira akan rufe duk makarantun kwana dake kauyaku.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng