APC: Za mu tabbatar da cewa abinda ya faru a Kankara bai sake faruwa

APC: Za mu tabbatar da cewa abinda ya faru a Kankara bai sake faruwa

- Jiya Shugabannin jam'iyyar APC suka tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa mulkin Buhari zai dage wurin tsare Najeriya

- Jam'iyyar ta ce gwamnati za ta kiyaye wurin tabbatar da cewa harin da aka kai Kankara bai maimaita kansa ba

- Jam'iyyar ta baiwa 'yan Najeriya hakuri, kuma ta tabbatar jami'an tsaro sun dage wurin basu isasshiyar kariya

A jiya shugabannin jam'iyyar APC, sun ce za su tabbatar sun rufe duk wasu gurbuna da za su janyo satar fiye da dalibai 300 na GSSS Kankara, a jihar Katsina bata maimaita kanta ba.

APC ta roki duk jami'an tsaron da ke kasar nan da su yi dubi a kan al'amarin da ya faru a Kankara, kuma a yi kokarin kiyayewa, Thisday live ta wallafa.

Jam'iyyar ta bai wa dalibai da iyayensu hakuri, inda ta tabbatar musu da cewa mulkin shugaba Muhammadu Buhari zai yi iyakar kokarinshi na tabbatar da ya samar wa dalibai hanyar karatu cikin kwanciyar hankali.

KU KARANTA: Yaran Kankara: Shehu Sani ya bai wa FG shawara a kan yadda za ta bai wa makarantu kariya

APC: Za mu tabbatar da cewa abinda ya faru a Kankara bai sake faruwa
APC: Za mu tabbatar da cewa abinda ya faru a Kankara bai sake faruwa. Hoto daga @Thisday
Asali: Twitter

An sace daliban a makarantarsu a ranar 11 ga watan Disamba, kuma an sako su 17 ga watan Disamba, bayan dagewa da kokarin gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina.

A ranar Alhamis, gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya sanar da nasarar ceto dalibai 344 daga hannun 'yan Boko Haram.

Shugaban jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya yaba wa Buhari da gwamna Masari bisa kokarinsu na ganin an sako daliban.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce kada Najeriya ta yarda 'yan ta'adda su dinga juyata. Ya fadi hakan ne lokacin da ya mika ta'aziyyarsa ga Sarkin Kaura Namoda, Alhaji Sunusi Muhammad Asha, bayan kashe hadiminsa da 'yan ta'adda suka yi yayin kai wa tawagarsa hari.

KU KARANTA: Satar yaran Kankara: Yunkuri ne na tozarta mulkina, Buhari

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matwalle na jihar Zamfara ya caccaki jam'iyyar APC a kan zarginsa da daukar nauyin ta'addanci a arewa maso yammacin kasar nan.

Idan ba a manta ba, satar daliban GSSS Kankara jihar Katsina, jam'iyyar APC ta yi zargin gwamnan PDP da kasancewa mai ruwa da tsaki a kan ta'addanci a arewa maso yamma.

Bayan jin hakan, gwamnan ya saki wata takarda, ta hannun mai bashi shawara a kan harkar labarai, Zailani Bappa, inda yace kame-kame kawai jam'iyyar take yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel