Rukayya Sulaiman: Mace ta farko matukiyar jirgin sama daga Katsina

Rukayya Sulaiman: Mace ta farko matukiyar jirgin sama daga Katsina

- Najeriya ta kafa tarihin zama kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta fara saka na'urar Level D Helicopter Full-Flight Simulator

- Ruqayya Suleiman, 'yar karamar hukumar Bakori da ta zama matukiyar jirgin sama ta farko daga jihar Katsina cikin wadanda PTDF ta dauki nauyi

- Rukayya tana daya daga cikin matuka jirgin sama da aka horar a South Africa, inda ta cika babban burinta na rayuwa tun tana karama

Najeriya ta zama kasa ta farko a nahiyar Afirika da ta fara saka na'urar Level D Helicopter Full-Flight Simulator, bayan Caverton da ta sanya nata na biliyoyin naira.

Ruqayya Suleiman ta kafa tarihi, inda ta zama matukiyar jirgin sama ta farko daga jihar Katsina, jaridar Katsina Post ta wallafa.

Ruqayya Suleiman 'yar karamar hukumar Bakori da ke jihar Katsina ta zama matukiyar jirgin sama ta farko daga jihar.

Rukayya Sulaiman: Mace ta farko matukiyar jirgin sama daga Katsina
Rukayya Sulaiman: Mace ta farko matukiyar jirgin sama daga Katsina. Hoto daga Katsinapost.com
Source: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace shugaban ma'aikata, sun halaka direbansa a Edo

Tana daya daga cikin matukan jirgin sama guda 15 da aka horar a South Africa cikin wadanda PTDF ta dauki nauyinsu a matsayin matukan jirgin sama wadanda za su iya zuwa ko ina a fadin duniya.

Kamar yadda mahaifin Ruqayya yace, babban burinta shine ta zama matukiyar jirgin sama, kuma bacin PTDF da ta dauki nauyin ta, da burinta bai cika ba.

Mahaifin Ruqayya ya bayyana farin cikinsa ta yadda diyarsa mai karancin shekaru ta kafa babban tarihi, musamman yadda al'ada take mayar da mata baya musamman a kan batun karatun gaba da sakandare.

KU KARANTA: Dalla-dalla: Yadda sojin Najeriya suka ceto 'yan makarantan Kankara

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta ce rundunar Operation Hadarin Daji ta kashe wasu 'yan bindiga, sannan ta kama wasu 2 sanye da kayan 'yan sanda, jaridar Leadership ta wallafa.

Kakakin rundunar sojin, Manjo janar John Enenche, ya ce rundunar yayin sintiri da daddare a ranar 17 ga watan Disamban 2020 suka ci karo da 'yan bindiga a Bakin ruwa a karamar hukumar Shinkafi dake jihar Zamfara, anan suka fara musayar wuta.

A cewarsa, sun kashe daya daga cikin 'yan bindigan, sannan sun kama 2. Sun samu nasarar kwace wata bindiga kirar AK-47, da kuma magazine a hannunsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel