Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace shugaban ma'aikata, sun halaka direbansa a Edo

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace shugaban ma'aikata, sun halaka direbansa a Edo

- Wani al'amari mai firgitarwa ya faru a Benin City, babban birnin jihar Edo a ranar Asabar

- Inda wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar

- Basu tsaya a garkuwa da Anthony Okungbowa ba, har kashe direbansa suka yi take a wurin

A ranar Asabar ne Benin City ta dauki zafi, inda wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Edo, Anthony Okongbowa, Newswire ta wallafa.

An yi garkuwa da Okongbowa, wanda gwamna Godwin Obaseki ya daura a mukamin HOS na jihar a watan Afirilu.

Wata majiya daga ma'aikatan gwamnatin jihar, ta tabbatar wa da Tribune Online, faruwar lamarin, amma sun bukaci a sakaya sunansu. Majiyar wacce ta tabbatar da yadda 'yan bindigan suka kashe direbansa, kafin su tsere dashi.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace shugaban ma'aikata, sun halaka direbansa a Edo
Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace shugaban ma'aikata, sun halaka direbansa a Edo. Hoto daga @Newswireng
Source: Twitter

KU KARANTA: Mu ne muka ceto yaran Kankara, Sojin Najeriya sun musanta ikirarin Gwamnoni da Miyetti Allah

An ce Okongbowa yaje wani taro ne inda suka lallabo suka sace shi.

"Yana hanyarsa ta komawa Benin City ne, bayan yaje wani taro da aka yi a Oza. An kashe direbansa," kamar yadda majiyar ta tabbatar.

Wani babban ma'aikaci, wanda yake da kusanci da HOS din, kuma yana aiki a ma'aikatar shari'a, ya tabbatar da yadda aka sace HOS din, kuma ya bukaci a boye sunansa, yace "Mun samu labarin, kuma gaskiya ne."

An yi kokarin kiran jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, sai dai bai ansa wayar ba.

KU KARANTA: Zargin daukan nauyin 'yan bindiga: Matawalle ya yi wa APC wankin babban bargo

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane 6, da wata mata tare da wasu yara 6 a wani hari na mayar da martani a karamar hukumar Kauru, bayan harin Zangon Kataf da aka kai ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba, daren Alhamis, 'yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Zangon Kataf dake jihar Kaduna, inda suka kashe mutane 7.

A wata takarda da kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan, ya ce gwamnatin tace a karkashin taimakon rundunar Operation Safe Heaven da 'yan sanda, sun tabbatar wa da gwamnatin jihar Kaduna cewa rikicin ya faru ne tsakanin makiyayan Kauru da karamar hukumar Lere.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel