Dalla-dalla: Yadda sojin Najeriya suka ceto 'yan makarantan Kankara

Dalla-dalla: Yadda sojin Najeriya suka ceto 'yan makarantan Kankara

- A ranar Asabar, rundunar sojin Najeriya ta bayyana yadda tayi ta ceto dalibai 344 na GSSS Kankara, jihar Katsina

- Kakakin sojin ya ce sai da sojojin suka yi ta bin dajin da 'yan ta'addan suka kai yaran cikin sando da buya

- Sun samu labarin yadda 'yan bindiga za su je kasuwa siyayya, sai suka yi amfani da damar suka kwaso yaran

A ranar Asabar rundunar sojin Najeriya ta bayyana yadda ta samu nasarar ceto dalibai 344 na GSSS Kankara, jihar Katsina a ranar 17 ga watan Disamba, Vanguard ta wallafa.

Ta bayyana yadda suka yi amfani da dabara ta musamman wurin ceto yaran ba tare da ji wa kowa ciwo ba, duk da yadda 'yan bindigan sukayi yunkurin kai wa rundunar hari.

Manjo janar John Enenche, kakakin rundunar soji da kuma tsohon shugaban rundunar soji ta musamman, sun bayyana hakan ne a ranar Asabar lokacin da ake hira dasu a gidan Talabijin na NTA.

KU KARANTA: Zargin daukan nauyin 'yan bindiga: Matawalle ya yi wa APC wankin babban bargo

Dalla-dalla: Yadda sojin Najeriya suka ceto 'yan makarantan Kankara
Dalla-dalla: Yadda sojin Najeriya suka ceto 'yan makarantan Kankara. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

NAN ta ruwaito yadda Jibrin, wanda yanzu haka hadimi ne na musamman ga ministan tsaro, manjo janar Bashir Magashi mai ritaya. Jibrin ya ce satar yaran ya sanya ministan tsaro ya jagoranci tafiyar, ciki har da shugabannin tsaro da hadimi na musamman ga shugabannin tsaro, zuwa Katsina da Kankara.

Ya ce ministan ya baiwa rundunar dokoki da tsarin da za su bi wurin ceto yaran ba tare da wasu sun cutu ba. Bayan sun shiga dajin, 'yan bindigan sun farga da hakan, sai suka kwashi yaran suka fara shiga can cikin dajin dasu.

"Duk da dai ba a ji wa wani cikin yaran ciwo ba, an kashe 'yan bindiga da dama, su kuma sojojin kara zurfafa cikin dajin suke. Sannan sun boye wurare daban-daban don dana wa 'yan bindigan tarko. Sun yi iyakar kokarinsu wurin kulawa kwarai, don kada su harbi wani cikin yaran."

Ya bayyana yadda rundunar da aka tura don aikin na musamman basu iya kyafta idanunsu ba, har ranar da suka ceto yaran.

Kamar yadda NAN ta ruwaito, sojojin sun samu labarin cewa 'yan bindigan za su je kasuwa siyayya, sai suka yi amfani da damar suka kwaso yaran tas, suka tsere dasu.

KU KARANTA: Matashiya mai kunar bakin wake ta tada bam, ta kashe mutum 3 a Borno

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta ce rundunar Operation Hadarin Daji ta samu nasarar ceto daliban GSSS Kankara guda 344 na jihar Katsina, The Cable ta wallafa.

Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara da Bello Masari, takwaransa na jihar Katsina sun ce kungiyar makiyaya shanu ra Miyetti Allah sune suka taka babbar rawa wurin ceto daliban.

Amma a wata takarda ta ranar Juma'a, kakakin hedkwatar tsaro, John Enenche, ya ce rundunar ce take da alhakin ceto yaran. A cewarsa, rundunar ta yi godiya ga jama'a musamman wadanda suka samar mu su da labaran da suka taimaka wurin ceto yaran.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel