Sojin Najeriya sun kashe tare da cafke 'yan bindiga a kayan 'yan sanda a Zamfara
- Hedkwatar tsaro tace rundunar Operation Hadarin Daji ta tabbatar da kama wasu 'yan bindiga a karamar hukumar Shinkafi
- Kakakin rundunar sojin, Manjo janar John Enenche ya tabbatar da hakan, inda yace an kama 'yan ta'addan sanye da kayan 'yan sanda
- Rundunar ta samu nasarar kashe daya daga cikinsu, sannan sun kama 2, sun kuma kwace miyagun makamai daga wurinsu
Hedkwatar tsaro ta ce rundunar Operation Hadarin Daji ta kashe wasu 'yan bindiga, sannan ta kama wasu 2 sanye da kayan 'yan sanda, jaridar Leadership ta wallafa.
Kakakin rundunar sojin, Manjo janar John Enenche, ya ce rundunar yayin sintiri da daddare a ranar 17 ga watan Disamban 2020 suka ci karo da 'yan bindiga a Bakin ruwa a karamar hukumar Shinkafi dake jihar Zamfara, anan suka fara musayar wuta.
A cewarsa, sun kashe daya daga cikin 'yan bindigan, sannan sun kama 2. Sun samu nasarar kwace wata bindiga kirar AK-47, da kuma magazine a hannunsu.
KU KARANTA: Ku daina karyar cewa zaman aure na da wahala, Leke Adeboye
Rundunar da aka tura Shinkafi, sun kama wata Zainab a ranar 18 ga watan Disamban 2020.
Ya ce an kama ta tana yawo cikin gari da kayan 'yan sanda.
Bincike ya nuna cewa Zainab ta dade tana yawo cikin gari tana damfarar jama'a da sunan ita 'yar sanda ce. Ya tabbatar da cewa an mika 'yan ta'addan a hannun hukuma don cigaba da bincike.
KU KARANTA: Rashin tsaro: An maka Buhari a gaban kotu saboda rashin sallamar shugabannin tsaro
A wani labari na daban, tsohon sanatan nan, Sanata Shehu Sani, ya bai wa jami'an tsaro hanyoyin kulawa da makarantu a arewacin Najeriya, Channels Tv ta wallafa.
Ya bayar da shawarwarin ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Asabar, bayan sace daruruwan daliban GSSS Kankara a jihar Katsina.
Sanata Shehu Sani, wanda ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya, yayi kira akan rufe duk makarantun kwana dake kauyaku.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng