Hotuna: Cike da farin ciki, iyaye sun hadu da 'ya'yansu da aka sace a Kankara
- Iyayen daliban GSSS Kankara sun share kwanaki basu hadu da yaransu ba
- Yaran sun yi matukar jigata bayan share kwanaki 7 a hannun 'yan bindiga
- Gwamnan jihar da shugaban kasa sun samu ganawa da daliban a sansanin mahajjata
Iyayen daliban GSSS Kankara na jihar Kaduna sun hadu da yaransu. An sace yaran ne a ranar 11 ga watan Disamba, kuma an sako su a daren Alhamis.
An mika su ga iyayensu a sansanin mahajjata da ke titin Daura a Katsina.
Daliban makarantar sun hadu da gwamnan jihar Katsina da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
KU KARANTA: Ma'auratan da suka shekara 72 sun rasu rana daya kuma a birnesu lokaci daya
KU KARANTA: Mu ne muka ceto yaran Kankara, Sojin Najeriya sun musanta ikirarin Gwamnoni da Miyetti Allah
A wani labari na daban, Gwamna Bello Matwalle na jihar Zamfara ya caccaki jam'iyyar APC a kan zarginsa da daukar nauyin ta'addanci a arewa maso yammacin kasar nan.
Idan ba a manta ba, satar daliban GSSS Kankara jihar Katsina, jam'iyyar APC ta yi zargin gwamnan PDP da kasancewa mai ruwa da tsaki a kan ta'addanci a arewa maso yamma.
Bayan jin hakan, gwamnan ya saki wata takarda, ta hannun mai bashi shawara a kan harkar labarai, Zailani Bappa, inda yace kame-kame kawai jam'iyyar take yi.
Kamar yadda yace, abin ban mamaki shine yadda babu kunya ba tsaron Allah, za a zarge shi da bata lokacinsa da kokarinsa har na tsawon sa'o'i 100, wurin tabbatar da an sako yaran.
Ya ce: "Wannan al'amarin yayi shige da na wata takarda da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya taba saki kwanakin baya, lokacin da gwamna Matawalle ya dage wurin ceto yara 26 na karamar hukumar Faskari, na nan jihar Katsina.
"Gwamna Matawalle ya dage wurin ganin ya kawo karshen ta'addanci a jiharsa. Kuma shugaba Buhari kullum cikin yaba masa yake yi. Yanzu haka jihar Zamfara tafi wasu makwabtanta zaman lafiya. Kuma ya yi alkawarin dagewa wurin ganin karshen ta'addanci a jiharsa."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng