Yaran Kankara: Shehu Sani ya bai wa FG shawara a kan yadda za ta bai wa makarantu kariya

Yaran Kankara: Shehu Sani ya bai wa FG shawara a kan yadda za ta bai wa makarantu kariya

- Sanata Shehu Sani ya bayar da shawarwari a kan yadda za a kawo karshen matsalar tsaro a makarantu

- A cewarsa, yakamata a samar da na'urar CCTV a kowacce makaranta, don kula da shige da fice

- Ya ce, ya kamata a horar da malamai da dalibai a kan hanyoyin sanar da hare-hare cikin gaggawa

Tsohon sanatan nan, Sanata Shehu Sani, ya bai wa jami'an tsaro hanyoyin kulawa da makarantu a arewacin Najeriya, Channels Tv ta wallafa.

Ya bayar da shawarwarin ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Asabar, bayan sace daruruwan daliban GSSS Kankara a jihar Katsina.

Sanata Shehu Sani, wanda ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya, yayi kira akan rufe duk makarantun kwana dake kauyaku.

Yaran Kankara: Shehu Sani ya bai wa FG shawara a kan yadda za ta bai wa makarantu kariya
Yaran Kankara: Shehu Sani ya bai wa FG shawara a kan yadda za ta bai wa makarantu kariya. Hoto daga @ChannelsTv
Source: Twitter

KU KARANTA: Rashin tsaro: An maka Buhari a gaban kotu saboda rashin sallamar shugabannin tsaro

Ya kuma bayar da shawara, inda yace ya kamata a hora dalibai da malaman makarantu don su san yadda za su yi idan wani rikici ko tashin hankali ya same su, cikin gaggawa.

Ya ce, ya kamata a sanya na'urar daukar hotonni ta CCTV, kuma su samar da hanyoyin sanar da matsalaloli cikin gaggawa a makarantun.

Shehu Sani ya nuna alhininsa a kan wadanda suke alfahari da samun nasarar ceto yaran, bayan babu wanda ya amince da cewa laifinsa ne rashin ceton manoman Zabarmari na jihar Borno da 'yan Boko Haram suka yi.

A cewarsa, ya kamata a ce shugabanni sun cire batun jam'iyya ko kuma ra'ayin siyasa, su yi kokarin taimakon kasar nan.

KU KARANTA: Mu ne muka ceto yaran Kankara, Sojin Najeriya sun musanta ikirarin Gwamnoni da Miyetti Allah

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matwalle na jihar Zamfara ya caccaki jam'iyyar APC a kan zarginsa da daukar nauyin ta'addanci a arewa maso yammacin kasar nan.

Idan ba a manta ba, satar daliban GSSS Kankara jihar Katsina, jam'iyyar APC ta yi zargin gwamnan PDP da kasancewa mai ruwa da tsaki a kan ta'addanci a arewa maso yamma.

Bayan jin hakan, gwamnan ya saki wata takarda, ta hannun mai bashi shawara a kan harkar labarai, Zailani Bappa, inda yace kame-kame kawai jam'iyyar take yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel