Ma'auratan da suka shekara 72 sun rasu rana daya kuma a birnesu lokaci daya

Ma'auratan da suka shekara 72 sun rasu rana daya kuma a birnesu lokaci daya

- Wasu suna cewa soyayya bata tsufa, tabbas hakan ne, don ga misali a kan Mama Esther da Baba Akojede

- Mama Esther wacce aurenta da Baba Akojede yayi shekaru 72, ta rasu bayan samun labarin mutuwarsa

- Kowa ya shaida irin kaunar da tsohon, mai shekaru 103 da matarsa mai shekaru 98, suke yi wa junansu

Sa'o'i kadan ne tsakanin mutuwar Baba Israel Akojede da matarsa Mama Esther, wadanda suka yi shekaru 72 da aure. An birne su a ranar Juma'a a makabartar Apostolic Faith Church da ke Ijeja a Abeokuta, jihar Ogun.

NANS ta ruwaito yadda ma'auratan suka mutu a ranar Juma'a, 30 ga watan Oktoban 2020 a Gbonagun, wuraren Obantoko da ke Abeokuta.

Kamar yadda NAN ta ruwaito, Israel yana da shekaru 103, yayin da Esther take da shekaru 98, inda ta mutu bayan samun labarin mutuwarsa.

Ma'auratan da suka shekara 72 sun rasu rana daya kuma a birnesu lokaci daya
Ma'auratan da suka shekara 72 sun rasu rana daya kuma a birnesu lokaci daya. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kankara: 'Yan bindiga da suka sace yaran makaranta suna tattaunawa da Miyetti Allah, Masari

Rev. Folorunsho Ajayi, babban faston coin Apostolic Faith Church da ke Ogun Regional Headquarters, Abeokuta, ya ce tare masoyan suke zuwa coci, kuma suna matukar kaunar juna.

Faston ya tunatar da yadda mata nagari, masu tsoron Ubangiji da kuma girmama mazajensu suke samun tsira.

Yayin da NAN ta tattauna da babban dansu, Joseph Akojede, ya bayyana iyayensu a matsayin masu matukar nuna kauna da kulawa ga juna.

"Sun ji dadinsu, duniya da lahira. Mutane ne masu kirki, ba wai don iyayena ne su ba. Suna son mutane," a cewarsa.

KU KARANTA: Fusatattun matasa sun banka wa barawon waya wuta a Oyo

Jikansu na farko, Olanreewaju Akojede, yace yana matukar jindadin yadda suka nuna masa so da kauna.

NAN ta tattauna da wasu makwabtansu a Odo-Ona Elewe dake Ibadan, sun bayyana irin soyayyar da suke nuna wa junansu.

A wani labari na daban, wani bidiyon amarya da ango wanda 'yan uwa da abokan arzikinsu suka yi ta manna musu N10 ya yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Bidiyon wanda 'yan Najeriya da dama suka yi ta cewa da alama ma'auratan basa yin farinciki da bikin.

Kowa yana tunanin dalilin da zai hanasu murna ranar aurensu, wasu cewa suke yi saboda N10 da ake manna musu ne, wasu kuma suna zargin auren dole ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng