Kai ne babban barawo; an fara tone-tone tsakanin Wike da tsofin kwamishinoni d suka koma APC
- An fara 'yar fallashe tsakanin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, da wasu tsofin kwamishinoninsa
- Gwamna Wike ya fusata ne bayan kwamishinonin sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
- Tsofin kwamishinonin sun mayar da martani a kan kalaman Wike na zarginsu da satar kudin gwamnati
Wasu tsofaffin Kwamishinoni guda biyu a jihar Rivers Ibinabo Michael-West da Dr John Bazia sun dawo da raddi akan kalaman Gwamna Nyesom Wike da ya bayyanasu a matsayin "farin shigan siyasa ko yara a harkar siyasa da kuma mutane masu halin ƙaranta".
Michael West ya yi aiki a matsayin kwamishinan Sufuri lokacin wa'adin mulkin Wike na farko, shi kuwa Bazia kwamishinan harkokin shuganci da al-umma ne.
Yayin wata ganawa da gidan talabijin a ranar Juma'a, tsoffafin kwamishinonin biyu waɗanda suka yi watsi da jam'iyyar PDP zuwa APC sun ce sun yi hakan ne bisa fushi da rashin jin daɗin zarginsu kan cewa sun wawure kuɗaɗen jihar.
Amma West, wanda shima ya yi magana a gidan Rediyo ranar Lahadi, ya ƙalubanci Wike da ya nuna hujjar cewa lallai ya saci kuɗin gwamnati zuwa Ajihunsa lokacin da yake aikin kwamishina.
"Na ƙalubalanci gwamnan jihar Rivers da ya kawo asusu na kai na da na yi amfani da shi wajen karɓar haraji, sannan ya kawo jadawalin kamfanonin da suka biya kuɗi asusuna da takardar shaidar yin hakan cikin awa 24 ga mutane jihar Rivers da ƴan Najeriya don su gani."
"Idan ba haka ba kuma zan tuntuɓi lauyoyina don ɗaukar matakan shari'ar da ya dace."
KARANTA: Bidiyo: An daura auren Suleiman da Ba-Amurkiyya, Jenine, a Kano cikin annashuwa
"Asusun da ake biyan haraji lokacin ina Kwamishina a bankin Heritage yake kuma hukumar haraji ce ta zaɓo asusun," a cewarsa.
Shi ma Bazia da yake magana a gidan rediyon 'Today Fm' a Port Harcourt ya ce Wike ba shi da wata shaida ko makama dangane da zargi.
"Kalli irin gidan da Wike ya ke ginawa a garinsu, shi kanshi gidan gari guda ne. Daga ina ya samu waɗannan kuɗaɗe? Har yana da bakin da zai buɗe ya kira wasu ɓarayi. To waye ɓarawon anan, a tsakaninmu?."
Legit.ng ta rawaito cewa Abdulrasheed Maina, ya yanke jiki ya fadi a gaban kotu yayin da ya bayyana a ranar Alhamis.
Yayin zaman kotu na ranar Laraba, Maina ya ce bai aikata laifin komai ba duk da cewa hukumar EFCC ta na yi masa tuhuma 12 a gaban kotu.
Kafin sake gurfanar da shi a gaban kotun ranar Laraba, Maina ya tsallake beli, ya sulale zuwa jamhuriyar Nijar.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng